TASKAR FALAQI DA NASI
TASKAR FALAQI DA NASI Darasi na Ukku-3 *Lokuta da wuraren da Annabi ﷺ ya Sunnanta mana karanta Falaqi da Nasi* 1-Wuri na Farko *Bayan kowace sallar farilla,ana karanta su sau daya,amma banda bayan sallar Assuba da Magriba,su ana karantawa ne sau Uku uku* Daga Uqbatu Bn Aamir R.A yana cewa: *"Manzon Allah ﷺ ya Umarce mu da muriqa karanta Falaqi da Nasi a bayan kowace sallah ya farillah"* @صحيح التمزي 2-Wuri na Biyu *Ana karantawa sau ukku uku,a safiya da yammaci* Daga Mu'azu bn Abdillahi bn Khabib daga Babansa yace: Mun fita a wani dare yana mana sallah sai muka nemi Manzon Allah ﷺ,a wani dare mai tsananin duhu,bamu gan shi ba,sai muka ganshi daga baya,sai yace: *(Fadi)*ban fadi komai ba,sai ya sake cewa;*(Fadi),amma bam fadi komai ba,sai ya sake cewa:*(Fadi)* sai nace mi zan fada?? Sai yace: *(Ka karanta Qulhuwa da Falaqi da Nasi sau uku-uku,duk lokacin da ka wayi gari ko kayi yammaci,sun isar maka daga dukkan komai)*. @أبي داود 3-Wuri na Ukku *Lokacin kwanciya barci,kafi