Amfanin Lemongrass ga Lafiya (Ciyawa- mai-kamshin-lemu)
Amfanin Lemongrass ga Lafiya (Ciyawa-
mai-kamshin-lemu)
Lemongrass (Cymbopogon citratus) shuka
ce mai dadin kamshi, wato wata irin
ciyawace doguwa mai launin kore da
kamshin lemun-zaki. Duk da yake dai bata
da alaka da lemun-zaki, kamshin ciyawar
mai karfi da dandano yayi kama dana
lemun-zaki (amma bata da zaki). Ana
samun ciyawar a kasashe masu yanayin
zafi ko yanayin dumi. Anfi yawan amfani
da ita a kasashen Asiya, Afurka da
Australia . Haka kuma, anfi yawan amfani
da wannan ciyawa a kasashen Asiya wajen
girki. A kasar Indiya kuwa akanyi amfani
da ita a matsayin maganin gargajiya (herb)
. Ana amfani da busassar ciyawar ko
danyarta domin amfani na daban-daban.
Kuma anfi amfani da ita wajen hada shayi
, miya ko kori (curry) domin ta zamo
hadin kayan kamshin girki. Ana samun
manta (lemongrass oil) a kasuwa wanda
shima ake amfani dashi na daban-daban.
Amfaninta:
Mai yiwuwa ne kana da wannan shuka a
gida ko a lambunka , koma kana amfani da
ita, to amma baka san ainahin amfaninta
taba ga lafiya, kawai dai ka dauketa shuka
ce domin k'awata gida, ko filebo maisa
kamshi a kofin shayin ka a lokacinda kake
kurɓawa. To ka bude idanunka, domin
kuwa wannan ciyawa amfaninta ya wuce
na adon gida kadai ko kamshin shayinka
da kake jin dadin sha saboda dandano da
kamshin da take baka a lokacin da kayi
amfani da ita. Ciyawar Lemongrass nada
ado da zata iya yima lafiyarka domin
inganta ta. Wasu daga cikin amfanin
wannan ciyawa mai albarka sun hada da:
1. Kariya daga ciwon-daji/kansa (Anti-
cancer). Shukar lemongrass nada sinadari
mai kamshi na "citral", wanda binciken
kimiyya ya nuna cewa yana kashe
kwayoyin halitta da ciwon kansa ya harba
a jiki (cancer cells). Haka kuma yana
inganta lafiyar kwayoyin halittar jiki gaba
daya (improving cellular health).
2. Karin-jini da hana rashin-jini (Anaemia)
. Lemongrass nada sinadarin "iron" mai
yawa, wato sinadari maisa karin-jini
domin cikakkiyar lafiya da kuma hana
wasu matsalolin rashin jini.
3. Rage hawan-jini (Reducing high blood
pressure). Yawan sinadarin "potessium" a
cikin lemongrass, sinadarin mai inganta
lafiyar zuciya, koda da sauran sassan jiki,
na taimakawa wajen hana hawan-jini,
cututtukan zuciya, mutuwar sashen jiki,
ciwo kansa, matsalolin rashin narkewar
abinci da rashin haihuwa, cikin yardar
Allah.
4. Kariya da hana girman kananan halittu
masu haddasa cututtuka a jiki (Anti-septic)
da kuma hana kumburi, wuri yayi ja, da
radadin ciwo a jiki (Anti-imflammatory),
musamman taimako ce ga masu ciwon
gabobi da sassan jiki da sauransu (gout,
arthritis, etc).
5.Yaki da cututtukan bakteriya dana
fangas (Anti-bacterial and anti-fungal).
Don haka, tana maganin zazzabin cizon-
sauro da taifot (Malaria and typhoid) [yi
shayi] , da sauransu. Haka kuma, tana
maganin cin-ruwa na yatsun kafa da
makero [yi amfani da manta] da sauransu
( athlete's foot, ringworm, etc).
6. Maganin mura, zubar hanci da hawaye,
kaikayin ido, atishawa, toshewar hanci
(Cold,flue and hay fever).
7. Tace duk wani abu mai guba ga jiki ,
musamman na abinci, ko wani abu mai
cutarwa da fitar dasu daga jiki
(Detoxifying). Tana tsaftace hanta, koda,
mafitsara da sauransu.
8. Inganta bacci / yakar da rashin bacci
(Fighting insomnia). lemongrass nada tasiri
wajen kwantar da hankali da fada da
rashin bacci domin samun cikakkiyar
lafiya.
9. Taimako ga masu ciwon-suga (Diabetes).
Tana rage yawan suga cikin jini, tsarkake
saifa da inganta aikinta.
10. Inganta kwalwa (Improving nervous
system). Lemongrass na taimakawa
kwalwa wajen maida hankali don lakantar
karatu, rike karatun da kuma taimakawa
wajen sarrafa karatun/ilimi. Sinadarin
"magnesium", "phosphorus" da "folate" da
ake samu a cikin ciyawar nada tasirin
kyautata lafiyar kwalwa.
11. Rage kiba (Weight loss). Shan
lemongrass musamman a shayi na
narkarda kitshe. Tana sanya yin fitsari
akai-akai a lokacinda take fitar da duk
wani abu mai yawa da jiki baya bukata
wanda zai iya cutar da lafiya.
Da sauransu.
Medical Disclaimer: Wanda ya rubuta
wannan bayanai ba likita bane, mai
bincike ne kawai akan magungunan
gargajiya, masani akan abinda ya rubuta
sakamakon bincike daya gabata. Wannan
bayanin amfanin ciyawar lemongrass da
duk kanin bayanan magunguna daya
wallafa a wannan shafin yanar gizo, baya
nufin masu matsalolin lafiya zasu iya
barin yin amfani da magungunan da aka
basu a asibiti ba domin su lazimci yin
amfani da maganin gargajiya, a maimakon
magungunan. A nemi shawarwarin likita
da masana ilimin maganin gargajiya akan
yanda za'a iya amfani da magungunan da
kuma sanin wanda zai iya amfani da
ciyawar da wanda bazai iya amfani da ita
ba wasu lokuttan.
Comments
Post a Comment