NISA'U AHLUL-JANNAH


🏞 Kalmar *"MACE"* tamkar *GOLD* ne ko kuma muce Sinadarin *ZINARI* mai yin *WALKIYA* a kowane *LOKACI* *MATA* Sunada wani *SINADARI*na *FARIN JINI* wanda yake da matukar Tasiri ga idon *MAZAJE* *MATA* Sunada matukar kima a Cikin Al'Ummah wadda har takai ga sun samu martaba da matsayi Babbah. *MATA* Sunada wani *LAUNI* mai Juya *MAZAJE* Tamkar Limzamin *DOKI* komai *MATSAYINKA* *MULKI, KUƊI* ko *SARAUTA MACE* sai ta Juya ka. *MATA* Sun Amsa Sunan Su *MATA* ga jan *AJI* da Juyin Juya Hali, komai Rashin Kyan *MACE* Kalma daya Zata sa *KASO* ta nan Take. *MATA* Sunada Hikima da Jurewa akan abunda suke matukar *SO* amman sai sukasa Nunawa. *MATA* Sunada Kunya, Hakuri da Juriya har sukan burgeka idan Ka Iya Zama Dasu. *MATA* Basu son mai kuntata masu koda yaushe sunfi son Mai kyauta ta masu. *MATA* Suna son *RAHA* da Abun *DARIYA* ko kuma Nishadantarwa. *MATA* Zuciyar su *FARA* ce tamkar farin *RUWA* ba wuya shawo kansu idan ransu ya Baci. *MATA* Sunada *HAKURI* da Tausayi da kuma Firgita akan wani abu Kadan. *MATA* Basa son, Saunan Mutum ko kuma ƙazamin Mutum. *MATA* Sunfi son mai *BASU* ako wane Lokaci da kuma nuna Tausayi agare *SU.* *MATA* Suna jajir cewa akan nuna *SOYAYYA* da Tausayin Junan. *MATA* Sunfi son mutum mai *HAKURI* da zafin nama har sukan yin Alfahari da Wannan. *MATA* Sunada Yauqi da son *DAULA* da kuma Anunasu Manya ne. *DARAJOJIN MATA GUDA (16) DA SUKA ƊARA MAZA! (USIKUM FIN NISA'I KAIRA)* Inai muku wasiyya da Alkairi ga mata "Inji Manzon Allah {s.a.w} a cikin Huɗubar Ban Kwana" *1- MACE CE* *TA FARA MUSULUNTA* a duk duniya kuma ta yiwa musulunci hidima da dukiyar ta da duk abinda ta mallaka harda GwalaGwalanta *(NANA KHADIJA) (R.A)* *2- MACE CE* Farkon wanda ta fara Istimbabi a cikin shari'ar musulunci........ *(NANA KHADIJA) (R.A)* *3- MACE CE* Sanadiyyar samun Taimama a shari'a *(UMMUNA A'ISHA) R.A* *4- MACE CE* Ta ilmantar da Sahabbai bayan wafatin Annabi{s.a.w} *NANA A'ISHA (R.a)* *5- MACE CE* Sanadiyar tsiran sahabbai daga fushin Allah sanda akai sulhun *HUDAIBIYYA* Kuma *MACE* ce ta shawo akan *SAHABBAI* har suka tsira daga fushin Allah. *(UMMU SALAMA) R.A* *6- MACE CE* Ta Kwantarwa Manzon Allah *HANKALI* Lokacin da Ifk ya faru a madina, kafin saukar wahayi *(BARIRA) (R.A)* *7- MACE CE* Wanda Manzon Allah *{S.A.W}* yace idan mutum ya tarbiyyantar da ita koda bashi ya haife ta ba, zai shiga *ALJANNA* shi da Manzon Allah *{S.A.W}* *8- MACE CE* Ta zamo Ma'auni damai Aure zai gwada kimarsa agun Mahaliccinsa, idan ya kyautata mata yanada sakamako mai kyau, idan kuma ya cuceta akwai uquba daga Allah. *9- MACE CE* Shari'a ta tanadar *MATA* Ladan Jam'im Salloli guda biyar (5) Da Juma'a da Jana'iza da Jihadi duk basai taje ba amma sanadiyyar ta Kyautatawa *MIJINTA* Allah Zai bata duk *LADAN* wadannan Ibadun. *10- MACE CE* Sanadiyyar warware matsalar Zahiri, suratul *(MUJADALA)* *11- MACE CE* Ta fara yin Sa'ayi tsakanin *SAFA da MARWA (HAJARA)* *12- MACE CE* Sanadiyyar tsiran mutanen sarauniyar Saba, suratl *(NAML)* *BILKISU MAI GADON ZINARI* *13- MACE CE* Sanadiyar musuluntar Sayyiduna Umar *(R.A) (FATIMA)* *14-,MACE CE* Ake samun nutsuwa da ita! *LITASKUNU ILAIHA* Namiji bazai taba samun sukuni ba sai yana da mace! *15- MACE CE* Duk mulkin mutum da dukiyar shi sai da ita yake kara kima a idon mutane! godiya nake. *Mata iyayen mune Mugirmamasu!*

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)