ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)
ASIBITIN ANNABI (SAW)
.
Idan BAQIN CIKI ne ya dameka, Ko Quncin
Rayuwa, Ko rashin Ciniki a Kasuwa, Ko Rashin jin
dadi awajen aikinka, Ko kuma MIJIN AURE kike
nema, to ga Wata Mafita daga Asibitin ANNABI
(S.A.W) :
.
- Yawaita Salati gareshi yana kawowa samun
biyan bukata da yayewar bakin ciki, da samun
farin ciki, Farin jini, da kuma daukakuwar
al'amuranka awajen Allah da bayinsa.
.
-Yawaita Istigfari yana kawowa gafarar Zunubai,
albarkar rayuwa, Bullowar hanyoyin arziki,
Toshewar kofofin Musibu, Yayewar talauci,
Bunkasar arziki, etc.
,
.
2. Idan Kuma al'amura ne suka chunkushe maka,
Makiya sun sakaka a gaba, Mahassada sun sa
maka ido, Suna ta Qulla Maka sharri da makirci,
To kyalesu ka kama Allah. Ka yawaita
"HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL"
.
Da ita ne Annabi Ibraheem (A.S) ya kubuta daga
sharrin Maqiyansa. Kuma da ita ne ANNABI
(S.A.W) da Sahabbansa suka samu kariya daga
sharrin Kafiran duniya alokacin da suka hada kai
domin rushe Musulunci daga doron Qasa.
.
- Ita kuwa "LA HAULA WALA QUWWATA ILLA
BILLAAHIL ALIYYIL AZEEM", Taska ce daga
taskokin gidan Aljannah. Don haka mai yawan
yinta ba zai, shiga Qunci ba. Kuma Mahassada
ba zasuyi nasara akansa ba.
.
3. Idan Jinya ce take damunka, ka rasa yadda
zakayi, To ka dauki addu'ar Annabi Ayyuba (A.S)
"(RABBI) INNI MASSANIYADH DHURRU WA ANTA
AR-HAMUR RAHIMEEN"
.
Zaka samu waraka da kuma yayewar chutarka
tare da ninninka maka Arzikinka da lafiyarka
(kamar yadda
akayi ma Annabi Ayyub din A.S.).
.
4. Idan kuma biyan bukata kake nema, ko
yayewar wani hali, ko neman shiriya daga halin
da kake ciki, to ka yawaita yin addu'ar Annabi
Yunus (A.S):
"LA ILAHA ILLA ANTA SUB'HANAKA INNEE
KUNTU MINAZ ZAALIMEEN".
.
Allah zai amsa maka kuma Zai yaye maka halin
da kake ciki. in sha Allahu.
.
.
5. Idan Kuma rashin samun Haihuwa ne, ko kuma
rashin Shiryuwar 'ya'yan da ka haifa, to ka
yawaita yin addu'ar Annabi Zakariyya (A.S):
"RABBI LA TADHARNEE FARDAN WA ANTA
KHAYRUL WARITHEEN".
.
.
6. Ya Allah ina rokonka da sunayenka Tsarkaka
da Siffofinka madaukaka Ka biya bukatun duk
wanda ya karanta rubutun nan Da wanda yayi
forwarding,
Da wadanda sukayi comment don
Soyayyar da Muke yiwa Annabinmu Muhammadu
(S.A.W).
#Hit share.
Allah ka karama Annabi daraja
ReplyDelete