TASKAR FALAQI DA NASI

TASKAR FALAQI DA NASI

Darasi na Ukku-3

*Lokuta da wuraren da Annabi ﷺ ya Sunnanta mana karanta Falaqi da Nasi*

1-Wuri na Farko
*Bayan kowace sallar farilla,ana karanta su sau daya,amma banda bayan sallar Assuba da Magriba,su ana karantawa ne sau Uku uku*

Daga Uqbatu Bn Aamir R.A yana cewa:
*"Manzon Allah ﷺ ya Umarce mu da muriqa karanta Falaqi da Nasi a bayan kowace sallah ya farillah"*
@صحيح التمزي

2-Wuri na Biyu
*Ana karantawa sau ukku uku,a safiya da yammaci*

Daga Mu'azu bn Abdillahi bn Khabib daga Babansa yace:
Mun fita a wani dare yana mana sallah sai muka nemi Manzon Allah ﷺ,a wani dare mai tsananin duhu,bamu gan shi ba,sai muka ganshi daga baya,sai yace:
*(Fadi)*ban fadi komai ba,sai ya sake cewa;*(Fadi),amma bam fadi komai ba,sai ya sake cewa:*(Fadi)* sai nace mi zan fada?? Sai yace:
*(Ka karanta Qulhuwa da Falaqi da Nasi sau uku-uku,duk lokacin da ka wayi gari ko kayi yammaci,sun isar maka daga dukkan komai)*.

@أبي داود

3-Wuri na Ukku
*Lokacin kwanciya barci,kafin a kwanta ana karanta su sau uku-uku tare da tofi sannan a shafa a sassan jiki gaba daya*

Daga Nana A'isha R.A tana cewa:
*"Manzon Allah ﷺ ya kasance a kowane dare idan yazo wajan kwanciya barcinsa,yana hada hannayansa gaba daya yayi tofi a cikin su,sannan ya karanta Qulhuwa,Falaqi da Nasi,Sannan ya shafi abinda ya saukaka na jikinsa,yana yin hakan sau uku"*

A wata riwayar:
*"Yana karantawa ne tare da yin tofi....."*
@البخاري و مسلم

4-Wuri na Hudu
*Lokacin rashin lafiya dan neman waraka ko Ruqya*

Daga Nana A'isha R.A tana cewa:
*"Manzon Allah ﷺ ya kasance idan baya da lafiya,yana karanta Quhuwa falaqi da Nasi,sai yini tofi a hannunsa,sai ya shafa a jikinsa, alokacin da rashin lafiya ya tsananta a gareshi,sai nake karanta masa na hada hannuwansa nayi masa tofi,sai na shafe masa jikinsa da hannunsa mai albarka"*

@صحيح الجامع

*Sharadin samun falala da Tasirin Falaqi da Nasi ga DAN adam*

Yana daga cikin abinda ya kamata mu fahimta wajan tasiri da amfanuwa da Falaqi da Nasi,shine lallai karanta wadan nan surori da sauran surorin Alqurani mai girma,yana da Alaqa da Imani da yarda da yakini na bawa ga Allah da kuma littafin Allah,sannan da yanayin karantun bawa.

Idan ka karantata da irin karatun Manzon Allah s.a.w tare da tunano ma'anar karantu da yin nazari akan ma'anonin ayoyinsu,tare da kyakkyawan niyya da kankantar da kai ga Allah da yarda da Abinda Manzon Allah s.a.w ya fada game da wadan nan surori masu albarka.

Wanda ya cika wadan nan sharudda shine yake ganin amfani da Tasirin wadan nan surori masu albarka da Izinin Allah.

Allah ne mafi sani.

Mu hadu a darasi na gaba Insha Allah.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)