AMFANIN ZOGALE GA JIKIN 'DAN ADAM

Zogale
(Moringa oleifera) itaciya ce mai ban
mamaki dangane
da amfaninta ga lafiyar 'dan adam. Allah
(S.W.T.) yasa albarka da waraka ga
wannan itaciya. Zogale abinci ne mai
romon sinadaran lafiya a bayan kasa,
baza'a iya kwatanta shiba da sauran
ganyaye ta fuskar amfaninsa ga lafiyar
'dan adam. Wannan dalili yasa wasu ke
kiransa da suna ITACIYAR RAYUWA ( The
tree of life). Ganyen zogale na kunshe da
romon
sinadari mai yawa na VITAMIN A (wanda
ke
karama idanun 'dan adam lafiya da gani)
fiye da
VITAMIN A dake cikin karas har sau 4.
Ganyen
zogale haka kuma yana da sinadari mai
yawa na
CALCIUM (mai sanya qashi da hakoran
'dan
adam kwari da lafiya) fiye da yawan na
cikin madara linki 4. Yana da sinadarin
VITAMIN C (wanda ke karfafa garkuwar
jikin 'dan adam domin fada da cututtuka
masu kai farmaki ga lafiyar mutum),
yanada wannan sinadarin mai yawa fiye
da irin
wannan sinadarin dake cikin lemu har
linki 7.
Haka kuma yanada sinadarin PROTEIN
(sinadari
mai gina jikin 'dan adam), fiye da na cikin
madara sau 2. Bugu da qari, yana da
VITAMIN E
(sinari mai gyara fata da lafiyar fata).
Masana ilimin kimiyya da bincike akan
wannan itaciyar lafiya sun bayyana cewa
ZOGALE/ZOGALA nada wadannan
magunguna:
-Yana daidaita sukari cikin jini.
-Yana rage hawan-jini
-Yana taimakama mace mai shayarwa da
ruwan nono.
-Yana kashe kwayoyin cutar bakteriya
(bacteria).
-Yana saukake narkewar abinci a ciki.
-Yana wanke ciki, musamman idan aka
cishi kafin aci komai.
-Yana kare lafiyar hanta da koda.
-Yana taimakawa da kuzari ga jikin
mutum.
-Yana rage kiba.
-Yana gyara kwalwa.
Da sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)