Amfanin Na'a-Na'a Ga Lafiyar Dan Adam ›
Na'a-na'a [Peppermint/mentha piperita or
mint] wata shuka ce mai albarka da ake
amfani da ita a matsayin maganin
gargajiya. Ganyen na'a-na'a kore ne,
kamshin ta nada karfi, tana da kamshi mai
dadin gaske da filebo mai sanyaya rai.
Na'a-na'a nada sinadarin 'minti' ( wato
'menthol') mai sanyaya rai da lafiyar jikin
dan adam. Akanyi amfani da na'a na'a
wajen sarrafa wasu kayan amfanin gida da
muke siya na yau da kullum, wato kayan
amfani da muke siya a kasuwa kamar
irinsu makilin (toothpaste), sabullai
(soaps), man-shafawa (creams and
vaselines), cingam (chewing gum),
sinadarin wanke baki (mouthwash) ,
magungunan shafawa (ointments), da
sauransu , saboda kamshinta da amfaninta
ga jikin dan adam.
Bincike ya nuna cewa, shukar na'a-na'a
dai ta samune asali ta hanyar auren-shuka
, wato auren shuka mai suna 'watermint'
da turanci da kuma wata shukar mai suna
'spearmint'. Bincike ya nuna cewa na'a
na'a tazo ne daga kasashen turawa da
larabawa. Mutanen wadannan kasashen da
muka ambata kanyi amfani da ganyen
na'a-na'a cikin abinci da kuma wajen
shayi, a matsayin ganyen-shayi (tea leaves)
haka kuma, akwai man -na'a na'a
( peppermint oil) da ruwanta (peppermint
water) a kasuwa domin amfani na daban-
daban.
Bincike ya nuna cewa na'a-na'a nada
amfani da yawa ga lafiyar dan adam. Wasu
daga cikin amfaninta ga jikin mutum sune:
1. Tana magance matsalar bacin-ciki da
rashin fitar bahaya maisa tsugunni
a bayi.
(Ayi shayin na'a-na'a ko azuba manta
cikin shayi marar madara.)
2. Tana saukake narkewar abinci
3. Maganin tuka
4. Maganin gudawa
5. Maganin mura da tari [da kuma mura
mai damun makoshi - wato 'sore throat']
(ayi amfani da man na'a-na'a ko ganyen ,
a tafasa ganyen ayi shayi marar madara
, haka kuma, za'a iya amfani da man na'a-
na'a cikin ruwan zafi, ayi turiri,
a lullube da mayafi).
6. Maganin ciwon-kai ( a shafa manta
wajen da kai ke ciwo).
7. Maganin ciwon-jiki ( a shafa manta ga
jijiyoyin jiki dake ciwo
ko wajen dake damunka da ciwo, zata
sanyaya, insha Allahu).
8. Maganin ciwon-hakori (ayi amfani da
man na'a-na'a da auduga,
a diga man ga auduga , sa'annan a lika ga
hakori mai ciwon).
9. Maganin kaikayi
10. Korar sauro ( a shafa man na'a-na'a ga
jiki -
hannuwa da kafafu , sauro zai gujesu)
11. Kashe tsutsar ciki
12. Taimakawa hanta wajen aiki
13. Rage yawan damuwa
- tana sanyaya rai da hana damuwa
( a tafasa ganyen
na'a-na'a ayi shayi, ko manta a zuba cikin
kofin shayi , safe da yamma).
14. Tana taimakawa kwalwa wajen rike
karatu da
kaifin fahimta (ayi shayi da ganyen na'a-
na'a a rinka sha da zuma).
15. Tana sanya girki yayi kamshi - filebo
( ayi amfani da ganyen wajen girki).
Hakan zai taimaka wajen son cin abincin
(appetite), musamman ga wanda
baya son cin abinci.
16. Tana maganin ciwon-ciki , musamman
ga mata masu matsalolin al'ada.
17. Da sauransu.
Comments
Post a Comment