DAGA CIKIN AIYUKA MASU SAUKI DA SUKE KAI MUTUM ALJANNA

DAGA CIKIN AIYUKA MASU SAUKI DA SUKE KAI MUTUM ALJANNA
                         

*1-kulawa da Maraya*

Annabi s.a.w yana cewa:
*(Ni da mai daukar nauyin Maraya a aljanna kamar haka muke,sai yayi nuni zuwa ga yatsarsa manuniya da ta tsakiya sai ya buda tsakaninsu)*.

@رواه.البخاري.

*2-Yin Zikiri bayan kare alwala*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Babu wani daga cikin ku da zaiyi alwala sannan ya kyautata alwalarsa, sannan bayan ya gama yace:*

{اشهد ان لاإله إلا الله وحده لاشريك له واشهد انا محمد عبده ورسو له}
Face an bude masa kokofin aljanna guda Takwas,yana shiga ta inda yaga dama).
@رواه.مسلم.

*3-Yin Sallar Assuba da La'asar acikin Jam'i*

Annabi s.a.w yana cewa:
*(Duk wanda ya sallaci Sanyi guda biyu"yana nufin sallar assubà da La'asar"ya shiga aljanna)*.

@البخاري.ومسلم.

*4-Kiyaye Salloli guda biyar na Farillah akan lokacinsu*

Annabi s.a.w yana cewa:
*(Dukkan wanda ya sallaci sallolin farilla akan lokacinsu,yana da alkawali awajan Allah ya shigar da shi Aljanna)*

@رواه.احمد.وابو.داود.والنسائي.

*5-Yin biyayya da kyautatama mahaifa*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Allah ya tumurmusa hancinsa har,(Allah ya tumurmusa hancinsa har,(Allah ya tumurmusa hancinsa har)sai akace wanene ya Manzon Allah??sai yace (wanda ya riski mahaifansa guda biyu ko guda daya bayan girma ya kamasu,sannan bai shiga Aljanna ba)*.

@رواه.مسلم.

*6-Kiyaye Harshe da al'aura*

Annabi s.a.w yace:
*(Wa zai kiyaye min tsakanin labbansa guda biyu"yana nufin harshe"da al'aurarsa,ni kuma zan lamince masa shiga aljanna)*

@رواه.البخاري.

*7-Yin Sallah raka'a biyu bayan alwala tare da,tare da halarto da zuciya lokacin sallar.*

Annabi s.a.w yace:
*(Babu wani musulmi da zaiyi alwala sannan ya kyautata alwalarsa,sannan yayi sallah raka'a guda biyu,ya fiskanci Allah acikin sallarsa da zuciyarsa da fuskarsa,face Allah ya bashi aljanna)*

@رواه.مسلم.

*Allah sanya mu a aljanna madaukakiya,ya bamu ikon aiwatar da Aiyukan alkhairi masu yawa*

Allah ne mafi sani.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)