WACCE IRIN ZUCIYA KAKE DA ITA?

_*WACE IRIN ZUCIYA KAKE DA ITA?*_

_Daga cikin zukatannan da Alla h s.w.t yakawo acikin ALQUR'ANI_

_*1. AL QALBUN SALIM*_
_Itce zuciyar da takeyin ayyukanta don Allah kuma ko kad'an babu 'bur'bushin ka'firci acikinta ko Muna'finci._

_*{ ﺇِﻟَّﺎ ﻣَﻦْ ﺃَﺗَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﺑِﻘَﻠْﺐٍ ﺳَﻠِﻴﻢٍ }*_

_*2. AL QALBUN MUNIYB*_
_Itace zuciyar da akoyaushe take mayar da al'amurranta ga Allah s.w.t kuma cike take da yawan tuba ga kuma d'a'a ga Ubangiji._

_*{ﻣَﻦْ ﺧَﺸِﻲَ ﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦ ﺑِﺎﻟْﻐَﻴْﺐِ ﻭَﺟَﺎﺀ ﺑِﻘَﻠْﺐٍ ﻣُّﻨِﻴﺐٍ }*_

_*3. AL QALBUN AL MUKHBIT*_
_Itace Natsatstsiyar zuciya mai shiru shiru._
_*{ ﻓﺘُﺨْﺒِﺖَ ﻟَﻪُ ﻗُﻠُﻮﺑُﻬُﻢْ}*_

_*4. QALBUN AL WAJAL*_
_Itace zuciyar da take fargabar cewa anyah ankar'bi ayyukan Alheri da nayi anya zantsira daga azabar ubangiji (wanda hakanne yake qa'ramata tsantseni)._

_*{ ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳُﺆْﺗُﻮﻥَ ﻣَﺎ ﺁﺗَﻮﺍ ﻭَّﻗُﻠُﻮﺑُﻬُﻢْ ﻭَﺟِﻠَﺔٌ ﺃَﻧَّﻬُﻢ ﺇِﻟَﻰ ﺭَﺑِّﻬِﻢْ ﺭَﺍﺟِﻌُﻮﻥ }*_

_*5. AL QALBUN ATTAQIY*_
_Atace zuciyar da take Girmama Dokokin Ubangiji._

_*{ﺫَﻟِﻚَ ﻭَﻣَﻦ ﻳُﻌَﻈِّﻢْ ﺷَﻌَﺎﺋِﺮَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻓَﺈِﻧَّﻬَﺎ ﻣِﻦ ﺗَﻘْﻮَﻯ ﺍﻟْﻘُﻠُﻮﺏِ }*_

_*6. AL QALBUN AL MAHADIY*_
_Itace zuciyar da ta sallama Al'amuranta ga Allah kuma ako yaushe take cikin yarda da duk wani hukunci na Allah s.w.t._

_*{ﻭَﻣَﻦ ﻳُﺆْﻣِﻦ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻳَﻬْﺪِ ﻗَﻠْﺒَﻪُ }*_

_*7. AL QANBUN AL MU'DIMA INNA*_
_Itace zuciyar da take cike da tauhidi da Anbaton Allah s.w.t._

_*{ ﻭﺗَﻄْﻤَﺌِﻦُّ ﻗُﻠُﻮﺑُﻬُﻢ ﺑِﺬِﻛْﺮِ ﺍﻟﻠّﻪ }*_

_*8. AL QALBUN AL HAYYU*_
_Itace zuciyar da takeyi aikin da iyakacin abinda tasani daga Alqur'ani da hadisi._

_*{ﺇِﻥَّ ﻓِﻲ ﺫَﻟِﻚَ ﻟَﺬِﻛْﺮَﻯ ﻟِﻤَﻦ ﻛَﺎﻥَ ﻟَﻪُ ﻗَﻠْﺐٌ }*_

_*9. AL QALBUN AL MARIYD*_
_Itace zuciyar da take fama da Rashin lafiya na kwankwanto ko munafinci da fa'jirci ko kuma rashin lafiyar da yake cusamata sha'awar haram._

_*{ﻓَﻴَﻄْﻤَﻊَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻓِﻲ ﻗَﻠْﺒِﻪِ ﻣَﺮَﺽٌ }*_

_*10. ALQALBUN AL A'AMAH*_
_Itace zuciyar da saidai tai ta kalle kalle Amma bata hango gaskiya kuma inma taga gaskiyar to bata wa'azantuwa da ita._

_*{ ﻭَﻟَﻜِﻦ ﺗَﻌْﻤَﻰ ﺍﻟْﻘُﻠُﻮﺏُ ﺍﻟَّﺘِﻲ ﻓِﻲ ﺍﻟﺼُّﺪُﻭﺭِ }*_

_*11. AL QALBUN LIL LA'HIY*_
_Itace zuciyar da ta gafala daga alqur'ani kuma tashagaltu da rud'in duniya da sha'awar duniya batare da lura da haqiqanin duniyar ba._

_*{ ﻻﻫِﻴَﺔً ﻗُﻠُﻮﺑُﻬُﻢْ }*_

_*12. AL QALBUN ASIYM*_
_Itace zuciyar da take 'boye shedar gaskiya._

_*{ﻭَﻻَ ﺗَﻜْﺘُﻤُﻮﺍْ ﺍﻟﺸَّﻬَﺎﺩَﺓَ ﻭَﻣَﻦ ﻳَﻜْﺘُﻤْﻬَﺎ ﻓَﺈِﻧَّﻪُ ﺁﺛِﻢٌ ﻗَﻠْﺒُﻪُ }*_

_*13. AL QALBUN ALMUTA KABBIR*_
_Itace zuciyar da tayi girman kai ga tauhidi da biyayya ga Allah._

_*{ﻗﻠْﺐِ ﻣُﺘَﻜَﺒِّﺮٍ ﺟَﺒَّﺎﺭٍ }*_

_*14. AL QALBUN GALIYZ*_
_Itace zuciyar da aka zarema tausayi da jin qai._

_*{ﻭَﻟَﻮْ ﻛُﻨﺖَ ﻓَﻈّﺎً ﻏَﻠِﻴﻆَ ﺍﻟْﻘَﻠْﺐِ ﻻَﻧﻔَﻀُّﻮﺍْ ﻣِﻦْ ﺣَﻮْﻟِﻚَ }*_

_*15. AL QALBUN AL MAKHTUM*_
_Itace zuciyar da bata sauraren shiriya kuma bata bin shiriya._

_*{ﺧَﺘَﻢَ ﻋَﻠَﻰ ﺳَﻤْﻌِﻪِ ﻭَﻗَﻠْﺒِﻪِ }*_

_*16. AL QALBUN AL QA'SIY*_
_Itace zuciyar da bata bin imani kuma bata tasirantuwa da duk wani abu da ake tasirantuwa da shi har imani ya qa'ru._

_*{ ﻭَﺟَﻌَﻠْﻨَﺎ ﻗُﻠُﻮﺑَﻬُﻢْ ﻗَﺎﺳِﻴَﺔً }*_

_*17. AL QALBUN AL GA'FIL*_
_Itace zuciyar da tayi sallama ga ambaton Allah kuma tatafi akan abinda rai keso sannan tariqa biyayya ga wanin Allah s.w.t._

_*{ ﻭَﻟَﺎ ﺗُﻄِﻊْ ﻣَﻦْ ﺃَﻏْﻔَﻠْﻨَﺎ ﻗَﻠْﺒَﻪُ ﻋَﻦ ﺫِﻛْﺮِﻧَﺎ }*_

_*18. AL QALBUN AL AGLIF*_
_Itace zuciyar da aka lullu6eta ta yadda saqon Manzon bazai shigetaba._

_*{ ﻭَﻗَﺎﻟُﻮﺍْ ﻗُﻠُﻮﺑُﻨَﺎ ﻏُﻠْﻒٌ }*_

_*19. AL QALBUN AL ZA'IG*_
_Itace zuciyar da take kaucema gaskiya._

_*{ﻓﺄَﻣَّﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻓﻲ ﻗُﻠُﻮﺑِﻬِﻢْ ﺯَﻳْﻎٌ }*_

_*20. AL QALBUN AL MURIYB*_
_Itace zuciyar da take za6in abinda take kwankwanto akanshi._

_*{ﻭَﺍﺭْﺗَﺎﺑَﺖْ ﻗُﻠُﻮﺑُﻬُﻢْ }*_

```YA ALLAH S.W.T KASANYA ZUKATANMU SUZAMA
KU'BUTATTU DAGA SHIRKA KUMA MASU YIN AIKI DON KAI```

_*✍🏽Malam Anas As-Salafy Fage*_

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)