YADDA AKE HADA MAN KWAKWA

YADDA AKE HADA MAN KWAKWA

Duba da dumbin amfanin da man kwakwa ke da shi wajen kula da lafiyar jiki, gyaran gashi da kuma fata, yana da amfani sosai a san yadda ake fitar da shi a gida, yadda ako da yaushe mutum zai iya kasancewa da shi a saukake.

Abubuwan da ake bukata
Kwakwa kamar guda uku ko fiye da haka
Ruwan mai dan zafi, ba zafi sosai ba
Yadda ake hadawa:-

-1. Za’a samu kwakwa a fasa ta a bambare ta daga kokonta, sai a wanke sosai a yayyanka kanana kanana yadda injin nika zai iya markadawa a saukake

-2. A dafa ruwan zafi, amma kar yayi zafin da zai iya kona jiki, kuma ya fi ruwan dumi zafi. Amfani da ruwan zafi na taimakawa wajan fitarda mai da yawa.

-3. Daga nan sai ki zuba yankakken kwakwan a cikin Blender ki kwara ruwan zafin, sai ki markada shi har yayi laushi. Idan kwakwar da yawa sai kin raba kamar gida biyu ko uku.

-4. Idan ya markadu, sai ki tace shi da rariya, ki mayarda dusar cikin Blender din ki kuma kara zuba ruwan zafi ki markada don ki samu karin madarar kwakwar.

-5. Ki kara tace madarar da rariyar laushi ko abin tace shayin domin fitar da kamu kamun dusar da ta ki fita da fari.

-6. Daga nan sai ki saka ruwan da kika tace a firji ya kwana. Da safe zaki ga man ya yo sama yayi fari sal a daskare abun sha’awa. Zaki ga ya raba kanshi da sauran ruwan kwakwan.

-7. Zaki tsame man sai ki tace sauran ruwan domin tabbatar da cewa duka man ne ya fita (kar ki zubar da ruwan, zaki iya dafa shinkafa da shi).

-8. Ki sanya man a cikin tukunya ki dafa shi na tsahon awa daya da kamar minti ashirin akan wuta mara zafi sosai (low heat). Zaki na yi ki na juyawa, kar ki bar gurin har sai ya yi.

-9. Idan yayi, zaki ga man ya rabu da dusar. Ki tace ci a cikin kwalba da dan karamin abun mataci. Idan bai tacu ba da fari, ki sake yi.

Za ki iya amfani da man kwakwarki wajen yin giki, gyara fata ko kuma gyaran gashi, ko kuma ki yi na sayarwa.



Danneman Karin bayani:- 08065444595

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)