Wata baiwar Allah ta haifi Yara 'Yan 4 a Jahar katsina


- Wata baiwar Allah ta haifi Yara 'Yan 4 a Jahar katsina

- Wani Dan siyasa dai ya tallafawa Matar da
kayan yara

- Sagir Malumfashi ya dauki dawainiyar suna
da sauran su
Kun ji cewa a farkon wannan makon wata
Baiwar Allah ta zubo yara ‘yan 4 a Garin
Malumfashi da ke Kudancin Jihar Katsina
kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar
nan ta Mikiya.

Sagir Malumfashi wajen matar da ta haifi
‘Yan 4 a asibiti
Tuni dai wani na kusa da mai girma
Gwamnan Jihar Katsina Mai Girma Aminu
Bello Masari watau Injiniya Muntari Sagir ya
dauki nauyin kayan suna da na dawainiyar
wadannan jarirai.

Sagir Malumfashi ya kai wa Matar data haifi
yan hudun tallafi a Unguwar Gora na Garin na
sa na Malumfashi a Ranar Talatar nan.

Wannan mata ta haifi maza uku ne dai da
kuma mace daya a lokaci guda a babban
Asibitin Garin na Kwandala.

Injiniya Sagir Malumfashi ya dauki dauyin
ragon suna da kuma kayan abincin yaran
wannan mutumi mai suna Malam Zubairu.

Honarabul din ya ba Mahaifiyar yaran
turamen atamfa tare da kudin kashewa.

Sai
dai an yi wannan mata addu’a don kuwa sai
dai aka yi mata aiki.

Muntari Sagir Malumfashi
ya taimakawa Matar da kaya.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)