WANI MAI HIKIMA YACE

WANI MAI HIKIMA YACE :Ba'a daure Kaya da wayau ko dubara dole Sai ansa igiya.

IKHLASI shine ginshikin karbuwar kowane irin aiki.

Kayi Don Allah Kuma kabari Don Allah sai Allah ya yi maka komi na alheri harda abinda Ka kasa.

Kazama Mai taimakon duk Wanda yake bukatar taimakon Koda ya taba saba maka Kuma kada Kazama Mai gori da naiman sakamakon alherin Ka a wajan mutane.

Badolene kowa yasoka ba domin kaima ba kowa kakeso ba Amma dolene Ka sauke ma kowa hakinsa Koda cikin wadanda ke kinka ne.

Mutunci ne babban ado ga kowane da nagari, kulum Ka nemi karuwar sa ba zubewar sa ba kada kayarda kazubar da mutuncin Ka saboda wani mutum domin in Mutuncin naka ya zube zai yar da Kai ya Nemo Mai mutunci.

Dama da karfi irin na duniya iri iri ne kada Kayi anfani da taka damar wajan taka wani domin bakasan wace irin dama Allah ya tanaza ma Wanda Ka taka a gobe ba, karka yarda Ka bata taka damar wajan sama ma wani tashi.

Yafiya da hakuri da kawaici sune mabudi na samun nasara da samun kowane Alheri.

Kyakyawan zato ga kowa na taimakawa wajan zama da mutane lafiya da Kuma samun masoya.

Idan Ka karanta wanan Kayi aiki dashi Kuma kayada ma wasu cikin abokan Ka da IKHLASI zaka Sami ladar Hakan a wajan mahalicin Ka Allah.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)