Tsohuwar jaruma, kuma shahararriyar jaruma a kamfanin shirya fina-finan Kannywood Mansura Isa ta ce ba ta jin damuwa akan rashin fitowa a fina-finai saboda sai da ta kai kololuwar ganiyarta kafin ta daina yin fim.

Tsohuwar jaruma, kuma shahararriyar jaruma a
kamfanin shirya fina-finan Kannywood
Mansura Isa ta ce ba ta jin damuwa akan
rashin fitowa a fina-finai saboda sai da ta kai
kololuwar ganiyarta kafin ta daina yin fim.

A cewar ta bata kewar bayyana a fim domin
sai da ta kai kololuwar ganiyar ta kafin ta bar
dandalin. Ta kara da cewa ta mallaki
muhimman abubuwa da kuma nasarori da
dama tace : "na gina gida na kaina, na sayi
mota, na je Umra, hasalima na auri gwarzon
jarumin Kannywood.
"Me zan ce bayan haka idan ba godiya ga Allah
ba", cewar Mansura a zantawa da ta yi da
jaridar yanar gizo na Premium Times.

Tsohuwar jarumar, wacce ta kasance edita ta
farko a masana'antar Kannywood, ta kara da
cewa ta daina fitowa a fina-finan ne lokacin
da ta yi aure saboda ta maida hankali ga
iyalinta.


A cewarta, yanzu ba ta kallon fina-finan
Kannywood saboda ba ta da isasshen lokaci
na yin hakan.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)