SOYAYYAR MANZON ALLAH (SAW).
SOYAYYAR MANZON ALLAH (SAWW).
*************************************
SON ANNABI (saww) wani hali ne ko dabi'a
wanda babu irinsa duk acikin halayen da
'Dan Adam zai iya siffantuwa dasu.
Zuciyar da aka tarbiyyantar da ita bisa son
Annabi (saww) takan Mance da duk wani
abinda ba SHI ba. Kuma bata iya yin wani
abu sai cikin koyi dashi.
Zuciyar da ta riga ta gaurayu da SON
ANNABI (saww) ta kan kasance batta ji, batta
gani sai da SHI. Kuma bata yin kowacce
Mu'amalar da zata nisantar da ita daga
gareshi.
Har ta kan kai matsayin yadda ba zata rayu
ba, sai da Tunaninsa (sallallahu alaihi wa
alihi wa sallam).
MISALI : daga cikin Sahabbai akwai
THAWBAAN (rta) wanda ya kasance ba ya
iya jin dadi arayuwarsa, har sai yazo ya kalli
Manzon Allah (saww).
Tsawon dare (Awa 12) yayi yawa agareshi.
Ba zai iya daurewa har gari ya waye bai ga
Annabi ba (saww).
Thawbaanu yakan kasa yin barci cikin dare,
har sai yazo ya kalli gidan da Manzon Allah
(saww) yake ciki.
* Sayyiduna KHALID BN WALEED (ra) ya
kasance ba ya iya yin barci har sai yayita
ambaton Manzon Allah (saww).
* Sayyiduna ABDULLAHI BN UMAR (ra) ya
kasance ba ya iya gudanar da komai hatta
tafiyansa, tsayuwansa, zamansa, cin
abincinsa, maganarsa, hawan dokinsa, sai
yayi irin yadda ya gani daga Manzon Allah
(saww).
Ya kasance bayan rasuwar Manzon Allah
(saww) yakan zo ya zauna akusa da Qabarin
Mai daraja, ya sunkuyar da kansa kamar
wanda yake magana da SHI (saww).
Sayyiduna BILAAL AL-HABASHIY (ra)
watarana yazo ziyartar Manzon Allah (saww)
bayan rasuwarsa... Sai da yazo gaban
Qabarin ya sunkuyar da kansa yana kuka..
Da ya hau kan mimbari yayi Kiran sallah
kuwa, SUBHANALLAH!!!! Sai duk garin
Madeena ya yamutse!!!
Kuka kakeji ko ta ko ina!!! Sahabbai Maza da
Mata, kowa sai kuka!!!!
Saboda wannan kiran sallar nasa, ya tuna
musu da Rayuwar Manzon Allah (saww).
Ya Allah ka Qara mana SON ANNABI (saww)
da iyalan gidansa da Sahabbansa.
Comments
Post a Comment