SIFFAR MUTUWA

SIFFAR MUTUWA

Mutuwa wata halittace mai zaman kanta, kuma ita kishiyar rayuwa ce dukkan mai rai baya sonta saboda dacinta da abubuwan dake biye da bayanta.

Mutuwa halittace mai girman gaske domin kuwa manzon Allah (SAW) yace lokacin da ubangiji ya halicci mutuwa saiya boyeta domin kada halittu su ganta. Ya boyeta da hijabi dubu sau dubu an kuma daure ta da sarqoqi dubu saba'in kowace sarka tsawonta ya kai tafiyar shekara dubu, babu wadansu mala'iku da suke iya kusantarta, kai babu Wanda ya San inda take balantana Susan a wane lokaci akayi ta.

A lokacin da ubangiji ya halicci mutuwa sai ya wakilta mala'ikan mutuwa a kanta sai mala'ikan mutuwa yace "Ya Ubangiji menene mutuwa? sai ubangiji ya umurci wannan hijabi ya yaye don mala'ikan mutuwa ya ganta, sai Ubangiji yace da sauran mala'iku kuma kuje kuyi kallon mutuwa, sai Ubangiji yace da mutuwa futo musu ki bude fuka fukanki da idanuwanki, lokacin da mala'ikun nan sukaganta sai duk suka suma har tsawon shekara  dubu lokacin dasuka farfado sai sukace ya Ubangiji ko ka halicci abinda yafi mutuwa girma?sai ubangiji yace nine na halicci ta kuma na fita GIRMA.

Sai Ubangiji madaukaki yace wa mala'ika Azara'ilu ka kama ta haqiqa na doraka a kañta, sai Azara'ilu yace ya Ubangiji banida qarfin da zani iya kamata.

Sai Ubangiji ya bashi qarfin da zai iya kamata, ya damqo ta da ta da hannunsa ya mallaqeta. Sai mutuwa tace ya Ubangiji kayi mani izini nayi kira sau daya a sama sai Ubangiji yayi mata izini, sai tayi kira da madaukakiyar murya tana cewa "nice mutuwa da ke raba tsakanin "ya"ya da iyayensu

Nice mutuwa da ke raba tsakanin yan'uwa, nice mai rusa katangu da benaye nice mutuwa dake raba tsanin mata da miji, nice mutuwa mai raya maqabartu, nice mutuwa da nake neman rai ido rufe koda kana kan bene mai tudu, babu wani abin halitta face sai ya dandane ni"

Kuma a cikin Alqur'ani mai girma Allah ta'ala yana cewa "kullu nafsin za'ikatil maut"

*
inda duk kuka kasance mutuwa zata riskeku

kuma koda kun kasan ce ne a cikin ganuwoyi ingantattu (suratul Nisa'i 78)

To yan uwa wannan itace mutuwa wadda Ubangiji ya jarrabi dan Adam da ita, domin ya nuna wanda yafi kyakkyawan aiki.kamar yanda Allah madaukakin sarki yake cewa:

اللذى خلق الموت والحيوة ليبلو كم ايكم احسن عملا  وهو العزيز الغفور.
Nine Ubangiji daya halicci mutuwa da rayuwa domin in jarrabi wannenku ne yafi aiki kyakkyawa nine nine mabuwayi mai hikima (suratul mulk aya ta 2)

Anan zan dakata sai Allah yasake sadamu

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)