NASIHOHI GUDA 30 DAN SAMUN I NGANTACCEN GIDA

NASIHOHI GUDA 30 DAN SAMUN I
NGANTACCEN GIDA

  NASIHA TA FARKO
"Zabar mace ta kwarai ko zabar miji na kwarai".

Babban foudation na gina rayuwar aure dan samun ingantaccen gida shine samun mace ta kwarai,wannan shine abinda Annabi s.a.w ya kwadaitar wajan aure.

Allah yana cewa:
(وَأَنكِحُوا الْأَيَامَىٰ مِنكُمْ وَالصَّالِحِينَ مِنْ عِبَادِكُمْ وَإِمَائِكُمْ ۚ إِن يَكُونُوا فُقَرَاءَ يُغْنِهِمُ اللَّهُ مِن فَضْلِهِ ۗ وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ )

( Kuma ku aurar da gwaurãye daga gare ku, da sãlihai daga bãyinku, da kuyanginku. Idan sun kasance matalauta Allah zai wadãtar da su daga falalarSa. Kuma Allah Mawadãci ne,Masani ).
@النور (32) An-Noor

Abune mafi kyau da shari'a ta koyar da dukkan mai neman aure ya zabi mace ta gari dan samun ingantaccen iyali da zasu gina al'ummar da Annabi s.a.w zaiyi alfahari da ita a gobe alqiyama.

Annabi s.a.w ya bamu labarin yadda mutane suke zabar mata wajan aure,sai yace:
(Ana auran mace ne saboda dayan abu hudu:Saboda kudinta ko saboda danginta ko saboda kyawunta ko saboda addininta,dan haka ka rabautuwa wajan zabar ma'abuciya addini,zaka rabauta).
@ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ.

Annabi s.a.w yana cewa:
(Duniya dukkanta wajan wani dan jin dadine kadan,amma mafi alkhairin jin dadin duniya shine;kasami mace takwarai).
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ 1468

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Mutum yayi kokari wajan samun zuciya mai yawan godiya ga Allah,da harshe mai yawan ambaton Allah da mace mumina wadda zata taimaka masa wajan samun lahirarsa).
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ " 5/282 " ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻭﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ ﻋﻦ ﺛﻮﺑﺎﻥ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ 5231

A wata riwaya yana cewa:
(...Ka sami mace saliha ta kwarai wadda zata taimaka maka wajan al'amuran duniyarka da lahirarka shine mafi alkhairi akan dukkan abinda mutane zasu tara maka).
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﻴﻬﻘﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ 4285

Manzon S.a.w yace:
(Ko auri mata wadanda suka iya soyayya da rike iyali kuma masu yawan haihuwa domin nayi alfahari da ku akan sauran al'umma).
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ ﻭ ﻫﻮ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻹﺭﻭﺍﺀ /6 195

Annabi s.a.w yace:
(Ku auri yan mata budurwa domin sunfi sauki mu'amala da amincewa da abu kadan da kuma saukin biyayya...).
Awata riwayar yana cewa:
(...saboda hidimarsu kadance kuma suna saurin biyayya).
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﺔ ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ 623

Mace ta kwarai daya ce daga cikin jin dadi da babban rabon duniya da samun cin nasara a duniya sai Manzon Allah yace:
(Yana cikin samun nasara da rabauta anan duniya samun mace ta gari,idan ka ganta zata sanya ka nishadi,idan baka nan zata gàre maka dukiyarka da ita kanta,yana cikin kuncin rayuwa kasami macen banza wadda idan ka kalleta zata baqanta maka kuma tana amfani da harshenta wajan cutar dakai,idan baka nan baka samun aminci tawajanta akan dukiyarka da ita kanta).
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻦ ﺣﺒﺎﻥ ﻭﻫﻮ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ 282

SHAWARA WAJAN ZABAR MIJI KO MACE AURE.

Annabi s.a.w ya bamu manyan shawara guda biyu wajan zaben miji ko matar aure,domin samun ingantaccen gida.

TAFARKO
Ga maza wajan zabar mace aure babban abinda zata dauka shine addini,domin shine abida Annabi s.a.w ya fada:
(....ka zabi ma'abuciya addini zaka rabauta).

Addini shi zata fara dubawa sannan dukkan wani quality ya biyo baya,amma da zarar an rasa addini to dukkan wani quality bazai sanya kaci nasaraba.

TA BIYU
A bangaran mace kuma sai Annabi s.a.w ya bata shawara wajan zabar miji sai yace:
(Idan wanda kuka amince da addininsa da halayansa yazo neman auranku to ku bashi aure,idan kun ki to fitina da fasadi mai yawa zai yadu a bayan kasa...).

Idan ka sami miji na gari na kwarai ya auri mace ta kwarai sai su gidana gida na kwarai wanda zai samar da al'umma ta kwarai wadda Manzon Allah s.a.w zai alfahari da ita a gobe Alqiyama.

Allah yana cewa:
(......وﺍﻟﺒﻠﺪ ﺍﻟﻄﻴﺐ ﻳﺨﺮﺝ ﻧﺒﺎﺗﻪ ﺑﺈﺫﻥ ﺭﺑﻪ ، ﻭﺍﻟﺬﻱ ﺧﺒﺚ ﻻ ﻳﺨﺮﺝ ﺇﻻ ﻧﻜﺪﺍ ......)
Allah ne mafi sani

Mu hadu a darasi na ga Insha Allah.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)