MAFARKI A MIZANIN SHARI'AH

*MAFARKI A MIZANIN SHARI'AH

.
Babu shakka fassara mafarki abu ne mai yiwuwa, domin kuwa ya tabbata tun daga zababbun halitta (Annabawa A.S.), zaka samu Annabin shine yayi, ko kuma wanine yayi shi kuma ya fassara masa.

.
Shaikh Dr. Ahmad Farid yace Za'a iya gane MAFARKIN gaskiya yayin da aka ga cewar ya nisanci wasu abubuwa marasa dadi, kamar: bakin ciki, firgici, kuncin zuciya, rudewa, sannan kuma ya samu dacewa da lokutan da muka ambata a (PART 1), kuma ya zamanto shi mai MAFARKIN ya kula da ladubban kwanciya, kamar tsarki, addu'oin kwanciya bacci d.s.s.

.
FALALAR MAFARKI MAI KYAU:
Manzon Allah(S) yace: "mafarki mai kyau ga mutum na gari yanki ne daga cikin yankin Annabta guda (46).
.

Mallam Bagwiy yace: don a girmama mafarkin ne, wasu kuma suka ce: asali Ilmin Annabawa ne sai aka baiwa mutumin kirki.
.

RABE-RABEN MAFARKI NA GARI:
Mallam Ibnul Qayyim ya ambaci guda (5) a littafinsa kamar haka:
.

1)- (ILHAMA) wanda zai jefa maka a cikin zuciyarka yayin da kake bacci.
2)- (MATHALUN) wanda Mala'ikan Mafarki yake bugawa azuciyar mai bacci, sai ka samu kansa cikin al'amarin tamkar da kai ake gudanarwa.

3)- (HADUWAR RUHIN MATACCE DA RAYAYYE) a yayin da kake bacci, sai ka samu kanka kuna tattaunawa da wani abokinka ko dan uwanka wanda ya mutu tamkar kuna a raye!

4)- (TASHIN RUHIN MUTUM ZUWA GA ALLAH) ta wannan hanyar sai Allah ya nunawa mai bacci wasu abubuwan na alkhairi.

5)- (SHIGAR RUHIN MAI BACCI CIKIN ALJANNAH) har ya zamto ka ga wasu abubuwan na ado da kawatarwa wanda suke ciki.
.

WANENE YA KAMATA YA FASSARA MAFARKI?........amsa tare da sauran wasu bayanan zai zo a (PART 3).
.

Allah ya nisanta mu daga MADAMFARA, sannan Allah ya karemu daga shiga abinda bamu da sani a cikinsa.
.

MADOGARA:
*Qur'an (12: 4, 36), (37: 103)
*Sahihul Bukhari (6/2563)
*Ar-Ruuh (41 - 42)
*Sharhus Sunnah (12/203 - 204).
.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)