MACE ABOKIYAR RAYUWA

MACE ABOKIYAR RAYUWA

*YIN WASA DA DARIYA DA ITA, JAN TA A JIKI DA SUMBATANTA*


🌺Tsokanar mace ayi wasa da dariya yana daga cikin abun da yake kawowa ma'aurata jin daďi da nishaďi. Kuma yana bada gudunmuwa wurin kawar da duk wani baqin ciki.

🌺Kamar yanda yazo a cikin hadisin da kowa ya sani cewa Manzon Allah (SAW) yana wasan tsere-tsere da Nana Aisha. Kuma yana yin musu duk wani abu da zai sanya su dariya da farin ciki. Ko saurayi ne idan yana yawan tsokanar budursa yana sata dariya to ko da ta rabu dashi zai yi wuya ta manta da shi. Duk sanda ta tuna kalmominsa sai ta hau yin dariya ko ta yi murmushi. Mace ana saye zuciyarta ta wannan fannin.

🌺Amma a san irin wasa da tsokanar da za a rinka yi domin akwai mazan da da su maka wasa gara ma sun bar shi domin rashin sanin muhallin tsokana, da irin ma tsokanar da zai yi. Namiji ya guji tsokanar mace da abun da ta nuna bata so ko take tsoro, domin ana tsokana ne don ayi wasa aji dađi ka ga tsokanar ta da abun da bata so sai dai ya bata ma ta rai tayi ta fushi.

🌺Jan mace a jiki kuwa yana sanya mace ta saki jiki da mijinta. Wato ba zata rinka kallonka kamar bako a gareta ba. Jan ta a jikinka zai rage mata yawan tsoro da shakka mara misaltuwa, sannan yana sanya sabo. Mace ta ji bama ta so namiji yayi nesa da ita domin koda yaushe yana manne da ita. Yazo a hadisi Annabi (SAW) yana kwanciya a kan cinyar Nana Aisha yana karatun alqur'ani Alhali tana haila.

🌺((عَائِشَةَ حَدَّثَتْهَا أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «كَانَ يَتَّكِئُ فِي حَجْرِي وَأَنَا حَائِضٌ، ثُمَّ يَقْرَأُ القُرْآنَ)).

🌺Haka kai ma zaka rinka mata, in tana zaune ka jawo ta jikinka, ko ka kwanta akan jikinta ko kirjinta ka taba nan ka taba can.

🌺Rungumar ta ma yana daga cikin jan ta a jiki, in tana kitchen tana aiki sai ka zo ta baya ka rungumeta ka sumbace ta. In zaka fita ko in ka dawo duka zaka iya yin mata domin shima yana sanya tausayi da kauna.

🌺Sai sumbatar ta, shima  yana da muhimmanci a zamantakewa, ya zama mace ta saba da sumban ka, ba wai ko yaushe bane zaka rinka mata irin su french kiss dss ba, a'a peck  ma ya isa. Shi ake so ka yawaita yin mata, kamar a kuncinta, goshinta, wuyanta, hannunta da sauran wurare. Sumbata da muke gani yana aika sako da yawa ga ma'aurata shi yasa ba a sake da shi. Nana Aisha tace Annabi (SAW) ya kasance yana sumbatan ta alhali yana azumi. Kun ga yanda Annabi yake nuna soyayyarsa ga iyalinsa. Wasu zaka ji sunce matan su basa son kissing đin su,  in sun kawo bakinsu sai su kawar da kansu, a nan cikin uku akwai ďaya:

🌺a. Ko dai ita ba mai son kiss ďin bace, domin akwai wacce kallon kazanta take ma kiss ba wai don mijinta na da matsala ba. Irin wannan ka ga peck shi ya kamace ta a hakura da sauran.


🌺b. Wata kuma kazantar bakin mijinta yasa bata iya yarda, domin sumba abu ne da yake bukatar tsafta, kada duk yanda bakinka yake kawai ka cambalawa mace baka tunanin cutarwar da zaka mata. Don haka a nan sai ka daure wajen tsaftace shi kafin ka kusance ta.

🌺c. Mouth ulcer (gembon ciki), waďanda suke da irin waďannan ciwukan to a gaskiya sai sun nemi magani. Domin komin brushing da zasu ma bakin su still zaka ji yana mutukar wari saboda daga cikinsu ne wari ke fitowa ba wai daga bakin ba. Irin wannan sai a nemi magani domin akwai su ana warkewa.

🌺Duka waďannan fa musulunci ne yazo dasu 'yan'uwa ba wai ďabi'ar yahudu bane. Sune suka sata a musuluncin mu, wani ma tun da ya auri iyalinsa bai taba sumbatarta ba. Shi komai na shi da isa da bunkasa yake yi, shi don me zai sake wa mace yana janta a jiki ta raina shi. Irin waďannan tunanin ne suke hana wasu nuna soyayyar su ga matan su. Ka koyawa mace sonka da son kasancewa da kai, ba wai a shimfiďa bane kaďai ake sace zuciyar mace ba. Wata ma idan kana shafata kana taba ta kullum zai zama kana ďauke 'kishin sha'awarta ba zata rinka damunka ba da yawa ba akan saduwa.  Namiji yana da kyau ya koyi dukkan abubuwan soyayya da jan hankali , sai mace ta kasa rabuwa da kai, ta kasa yin maka rashin mutunci domin ta san in ka kufce mata samun irinka sai an duba. Amma in ka zama bagidaje a wurin iyalinka sai ta raina ka, kuma ka daina mata kwarjini domin bata same ka yanda take so ba.

*Rubutun jiya shine na 25 nayi mistake na sa 26.*

🌺 *'Yar'uwa ku Sadeeya Lawal Abubakar.*

🌺 *MARKAZUS SUNNAH*

🌺 *Zaku iya shiga group din ta wainnan numbers din 08034643244 08089074217*

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)