*LABARIN SOYAYYA* Soyayyar Annabi na nake nufin in gaya muku, ba soyayyar wani ko Wata ba…

LABARIN SOYAYYA

Soyayyar Annabi na nake nufin in gaya muku,
ba soyayyar wani ko Wata ba

.
.

TSANTSAR SOYAYYA : ita ce lokacin da Masu
kudi da dukiya suka fito suna son Nana
Khadeeja (ra) amma ta Qisu tace ita
MUHAMMADUR RASULULLAHI takeso.

.

kuma bayan ta aureshi sai ta hakura da komai
na duniya.. Ta zama ita ce Khadimar Ma’aiki
(saww) ta farko tun kafin Annabta..
.
Ta mallaka masa dukkan Miliyoyin dukiyarta

.
.
TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da
Sayyuduna Zaidu bn Harithata (ra) ‘Yan
uwansa suka zo domin su fansheshi daga
bauta, Sai yace musu A’a shi ya gwammaci ya
zauna amatsayin bawa awajen Manzon Allah
(saww) maimakon ya koma garinsu.

.
TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da
Manzon Allah (saww) yasha ruwa daga cikin
wata Gora agidan Ummu Sulaym (ra) sai ita
Ummu Sulaim din ta tashi ta yanke bakin
gorar daidai wajen da bakin Manzon Allah
(saww) mai daraja ya ta’ba, ta ajiyeshi domin
neman albarkarsa (SAWW).

.
.
TSANTSAR SOYAYYA : ita ce lokacin da Abu
Turab Wato Shugaban Sadaukai, Imam Aliyu
Bn Abi Talib (rta) ya yarda ya amince ya
kwanta akan Shimfidar Ma’aiki (saww) acikin
daren da Mushrikai suke nufin su kasheshi..

.
Ya yarda ya kwanta amadadinsa, duk da
yasan cewa zasu iya harbinsa da kibiya ko su
kasheshi tun kafin su gane cewa ba Ma’aikin
bane awajen. (saww)

.
.
TSANTSAR SOYAYYA ITA CE : Lokacin da
Bilal Al-Habashiy ya dena kiran sallah tun
daga ranar da Ma’aiki ya bar duniya!!
.
Bilalu (rta) bai Qara yin kiran sallah ba… Sai
rannan Sayyiduna Umar (ra) yace masa yazo
yayi (aranar da aka karbo Masallacin Qudus).

.
Da Bilalu ya fara kiran sallah, yazo daidai
wajen “ASH-HADU ANNA MUHAMMADAR
RASULULLAH!! Yana fada haka, sai ya fashe
da kuka, Sahabbai ma kowa sai kuka

.
An ce ba’a ta’ba ganin ranar da daruruwan
Sahabbai sukayi kuka suka zubar da
hawayesosai kamar wannan ranar ba… Sai
sukaji Tamkar awannan lokacin ne Ma’aiki ya
bar duniya!!

.
.
TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da
Manzon Allah (saww) yazo gidan Sayyiduna
Abubakrin (ra) yace masa “ALLAH YA
UMURCENI INYI HIJIRA”.
.
Sai Sayyiduna Abubakar yace “Ina fatan tare
dani zaka tafi?” Sai Ma’aiki yace masa
KWARAI KUWA. ALLAH YACE MUN IN TAFI
TARE DAKAI”.

.
Sai Sayyiduna Abubakar ya fashe da kuka don
murna!!! Allahu Akbar!!!

.
TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da
Manzon Allah (saww) ya kwanta barci akan
cinyar Sayyiduna Abubakar (ra) alokacin da
suke cikin Kogo.. Sai Sayyiduna Abubakar ya
rika yagar rigarsa yana tottoshe ramukan da
suke cikin kogon. Amma duk da haka akwai
sauran wani rami wanda bai samu abin
tosheshi ba.

.
Chan sai ga wani Maciji ya leko ta cikin
wannan ramin yana so zai fito. Don haka sai
Sayyiduna Abubakar ya sanya Qafarsa ya
toshe ramin don kar Macijin nan ya fito ya
chutar da Manzon Allah (saww).

.
Macijin nan yayi ta cizonsa yana zuba masa
dafi. Amma duk da haka bai motsa ba, don
kar ya tashi Manzon Allah (saww).

.
TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da
Manzon Allah (saww) ya tambayi Khadiminsa
wato Sayyiduna Rabee’atu bn Ka’ab (ra) :

MECECE BUKATARKA?”.

.
Sai yace : “MAKOBTAKA DA KAI NAKE SO
AGIDAN ALJANNAH”.

.
TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da wata
Mata Mijinta da Mahaifinta da ‘Dan uwanta
duk suka yi shahada awajen Yaqin Uhudu,
Mutane suna yi mata Ta’aziyyah amma bata
sauraresu ba..

.
Ita dai tana tambayar yaya Manzon Allah
(saww) yake?? Da aka kaita wajensa, ta
ganshi sai tace : “DUK WATA MUSIBAH AI
QANKANUWA CE BAYAN KAI YA
RASULALLAHI!! (Wato rashinka shine Babban
Musiba. Amma tunda kana nan da ranka, to
babu damuwa Ya Ma’aikin Allah!!

.
TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da
Manzon Allah (saww) yaga Sahabinsa mai
suna Thawbanu duk launin fuskarsa da jikinsa
ya chanza. Sai ya tambayeshiMENENE YA
SAMEKA YA THAWBANU?”.

.
Sai yace : “Ya Rasulallahi wallahi babu rashin
lafiya ko Jinya tare dani. Sai dai ni idan ban
ganka ba, ina shiga cikin wani mawuyacin
hali. Har sai nazo na kalleka tukunna!”.

.
TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da
Abdullahi bn ‘Ubayy bn Salul ya fadi bakar
Magana akan Manzon Allah (saww) nan take
saiDansa ya zare takobi zai kasheshi..

.
Yace: “Kaine Makaskanci. Kuma idan ka
maimaita abinda ka fada wallahi sai na
kasheka!!”.

.
.
TSANTSAR SOYAYYA : ita ce lokacin da
Manzon Allah (saww) yace “KADA KU CHUTAR
DANI ACIKIN LAMARIN A’ISHA”. (Wato idan
kuka chutar da ita, to ni kuka chutar).
.

TSANTSAR SOYAYYA : Ita ce lokacin da
Manzon Allah (saww) ya rika hannun Imam
Hasan da Imam Husaini, sannan yace : “DUK
WANDA YASO WADANNAN GUDA BIYUN NAN,
SANNAN YASO MAHAIFINSU DA
MAHAIFIYARSU, TO YANA TARE DANI AGIDAN
ALJANNAH”.

.
Kuma yace “Ya Allah ina son Alhusaini. Ya
Allah kasoshi, kuma kaso duk mai sonsa”.

.
Manzon Allah (saww) yace “MAFIYA
SOYAYYATA ACIKIN AL’UMMATA, WASU
MUTANE NE WADANDA ZASU ZO ABAYANA.

‘DAYANSU ZAI YI BURIN YA BAYAR DA
IYALANSA DA DUKIYARSA DOMIN YA SAMU
GANINA”.

.
Ya Allah kasa MU-NE!! Ya Allah kasa MU-NE!!
Ya Allah kasa MU-NE!!.

.
Anan zamu tsaya sai wani karon kuma.. Zamu
ci gaba InshaAllahu.

.
Ya Allah yi salati da aminci bisa Annabinmu
Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka
da Sahabbansa da dukkan Masoyansa tare
damu baki daya.

Allah yakarama son Annabi muhammadu s.a.s

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)