KUSA-KURAI GUDA 13 GAME DA SALLAR JUMA'A DA RANAR JUMA'A*_

*KUSA-KURAI GUDA 13 GAME DA SALLAR JUMA'A DA RANAR JUMA'A*_

➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖

_Ranar juma'a tana cikin ranaku mafi falala Awajan *Allah*. Kamar yadda hakan ya tabbata a Hadisi Sananne daga *Manzon Allah s.a.w:*_

_*(Mafi Alkhairin Yini wanda Rana take fitowa a cikinsa Shine Ranar Juma'a. A Yinin ne Aka Halicci Annabi Adamu, kuma a yinin ne aka shigar da shi Aljanna, kuma ayinin ne Aka fitar da shi daga cikinta)*_

@ ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ .

_Mafi yawan mutane suna Aukawa cikin kusakurai masu girma game da Sallar Juma'a da Ranar Juma'a. Ga kadan daga cikinsu:-_

_1-Rashi Qudurta Niyya a Zuciya Lokacin tafiya Sallar Juma'a. Mafi yawa sun dauki tafiya Zuwa Masallacin a Matsayin Al'ada Alhali tafiyar zuwa Masallacin Juma'a Ibadace mai Zaman kanta mai Lada da Yawa da Falala._

_*Annabi s.a.w* Yana Cewa: (Dukkan Aiyuka sai da Niyya suke tabbata kuma ko wane mutum da abinda yayi niyya)._

_Tafiya Zuwa Masallaci Kowane taku kana Samun ladar Azumi da Raya Dare kamar yadda Abu dauda ya fitar da shi albany ya ce hadisine hasan._
_*@Saheehul jami'i*_

_Amma wanna ladar babu wanda zai sameta sai wanda yayi niyyar tafiya ya Zuwa Sallar Juma'a ._

_2-Rashin Halartar zuwa Sallah Juma'a dan kasala ko sakaci ko da Gangan._

_Rashin zuwa sallar juma'a babu wani dalili da shari'a ta amince, laifine daga cikin manyan laifuka._

_*Manzon Allah s.a.w* yana cewa: (Ko dai mutane su daine rashin zuwa sallar juma'a, ko kuma *Allah* yayi rufi a zukatansu su zama daga cikin gafalallu)._

@ ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ .

_*Manzon Allah s.a.w* yana cewa: (zuwa sallar juma'a wajibine akan kowane musulmi,in banda mutum hudu: *Bawa wanda aka mallaka,* ko *mace* ko *yaro karami* ko *marar lafiya* )._

@ ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ .

_3-Kebe Daren juma'a da wata ibada ta musanman indai ba yawaita salati ga *Manzon Allah s.a.w* ba. Da rashin halartar sallar Asuba ta ranar juma'a cikin jam'i._

_Babu wata ibada ta musamman da aka kebe daren juma'a da ita a sunnar *Annabi s.a.w* ingantacciya in banda yawaita salati ga *Annabi s.a.w*._

_*Annabi s.a.w* yana cewa: (Ku yawaita yi min salati mai yawa a Ranar Juma'a da Daren juma'a, hakika duk wanda yayi min Salati daya, to *Allah* zai yi masa goma)._

@ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﻴﻬﻘﻲ ﻭﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ .

_Kuma sallar Asubar anar Juma'a itace Sallah mafi falala da matsayi a wajan Allah acikin dukkan salloli._

_*Annabi s.a.w* yana cewa:(Mafificiyar sallah a wajan *Allah* itace sallar Asubar Ranar juma'a a cikin jam'i)._

@7/207 ‏) ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ
ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ : 1566 .

_Ba karamar Asara bace Mutum yaki halartar sallar Asuba ta Ranar Juma'a a cikin jam'i._

_4-Rashin Zuwa Masallaci da wuri dan sauraran Huduba. Sai kaga mutum yazo lokacin ana Huduba ko gab da fara sallah._

_Abu ne Sananne zuwa Masallaci da wuri dan Sauraran Huduba da kuma yin shiru lokacin Huduba yana cikin wajiban sallar juma'a, kamar yadda zuwa da wurin yana da lada ta Musamman._

_*Annabi s.a.w*  yana cewa: (Idan Juma'a tazo, a kan kowace kofa daga cikin kofofin masallaci akwai mala'iku suna rubuta wanda yazo na farko da wanda yazo bayansa, idan liman ya hau kan mibanri sai su rufe takardunsu su saurari Huduba, wanda yayi kokarin zuwa a farkon lokaci yana da ladar kamar wanda yayi sadakane da raqumi sannan saniya sannan rago sannan kaza sannan kwai)._

@ ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ .

_5-Rashin yin Wankan Juma'a da sanya turare da yin aswaki da sanya tufafi mai kyawu._

_*Annabi s.a.w* yana cewa: (Wankan juma'a wajibine akan dukkan wanda ya isa mafarki"wato wanda ya balaga")._

@ ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ .

_*Annabi s.a.w* yana cewa: (Idan dayanku zai zo sallar juma'a to yayi wanka)._

@ ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ .

_*Annabi s.a.w* yana cewa: (Wanda yayi wanka a ranar juma'a ya sanya turare daga cikin turaran iyalinsa idan suna dashi,ya sanya mafi kyawun tufafinsa,sannan ya tafi zuwa masallaci, yayi raka'a shiga masallaci idan da dama sannan bai cutar da wani ba,sannan yayi shiru lokacin da liman ya fito har aka gama sallah, An gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa daga wannan juma'ar zuwa wata juma'a)._

@ ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ .

_7-Saye da sayarwa bayan anyi kiran sallah na biyu Ranar juma'ah._
_*Allah* yana cewa:_

( ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﺇِﺫَﺍ ﻧُﻮﺩِﻱَ ﻟِﻠﺼَّﻠَﺎﺓِ ﻣِﻦ ﻳَﻮْﻡِ ﺍﻟْﺠُﻤُﻌَﺔِ ﻓَﺎﺳْﻌَﻮْﺍ ﺇِﻟَﻰٰ ﺫِﻛْﺮِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺫَﺭُﻭﺍ ﺍﻟْﺒَﻴْﻊَ ۚ ﺫَٰﻟِﻜُﻢْ ﺧَﻴْﺮٌ ﻟَّﻜُﻢْ ﺇِﻥ ﻛُﻨﺘُﻢْ ﺗَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ )

_*( Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan anyi kirã zuwã ga salla a rãnar Jumu'a, sai ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar ciniki. Wancan ɗinku ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani)*_

@ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ‏( 9 ) _Al-Jumu'a_

_Idan anyi kiran sallar juma'a na biyu saye da sayarwa ya zama haramunne abisa dalilin wannan ayar._

_*Allah* Ne Mafi Sani_

_*✍🏼Mustapha Musa*_

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)