KASAN ADDININ KA???

KASAN ADDININ KA???

.
@Karatun Fighu daga cikin Littafin Hallul masa'il

.
‏« ﺃﻗﺴﺎﻡ ﺍﻟﻤﻴﺎﻩ ‏»

«RABE-RABEN RUWA»

.
.
(( ﺍﻟﻤﻴﺎﻩ ﺛﻼﺛﺔ :))

((SHI RUWA YA KASU GIDA UKU))

.
.
١ - ﺍﻟﻤﺎﺀﺍﻟﻤﻄﻠﻖ :

1-RUWA MUDLAKI, (shine Ruwa mai tsarki kuma mai Tsarkakewa)

.
« ﻭﻫﻮﻣﺎﻟﻢ ﻳﺘﻐﻴﺮﻟﻮﻧﻪ،ﺃﻭﻃﻌﻢ
ﻩ،ﺃﻭﺭﻳﺤﻪ،
ﺑﺸﻰﺀﻃﺎﻫﺮﺃﻭﻧﺠﺲ،ﺃﻭﺗﻐﻴﺮﺑﻤﺎ ﻓﻰ ﻗﺮﺍﺭﻩ ﺃﻭﺑﻄﻮﻝ ﺍﻟﻤﻜﺚ »

.
«SHINE RUWAN DA LAUNIN SA, ko DANDANON SA, ko KAMSHIN SA BASU CANZA BA, DA WANI ABU MAI TSARKI ko NAJASA, KODA YA CANZA SABODA TABBATAR SA A GURI (kamar Kasar gun mai gishi ce) ko SABODA TSAWO ZAMAN SA» (ya haifar da Gansa kuka)

.
« ﻳﺴﺘﻌﻤﻞ ﻓﻰ ﺍﻟﻌﺎﺩﺍﺕ ﻭﺍﻟﻌﺒﺎﺩﺍﺕ »

«ZA'AI AMFANI DA WANNAN RUWAN WAJAN MU'AMALA ko IBADA»

.
٢ - ﺍﻟﻤﺎﺀﻃﺎﻫﺮ .

1-RUWA MAI TSARKI (Wanda baya Tsarkakewa)

.
« ﻭﻫﻮﻣﺎﻳﺘﻐﻴﺮﺃﺣﺪﺃﻭﺻﺎﻓﻪ ﺍﻟﺜﻼﺛﺔ،ﺑﺸﻰﺀﻃﺎﻩﺭﻳﻐﺎﺭﻗﻪ ﻏﺎﻟﺒﺎ،ﮔﺎﻟﺰﻳﺖ،ﻭﺍﻟﻠﺒﻦ،ﻭﺍﻟﺴﻤﻦ،ﻭﻏﻲ
ﺭﻩ »

«SHINE RUWAN DA DAYA DAGA CIKIN SUFFOFIN SA UKU SUKA JIRKITA, DA WANI ABU MAI TSARKI, WANDA SAUDA YAWA AKE RABE SU DASHI kamar MAI,ko NONO, ko KITSE» da dai sauran su.

.
« ﻳﺴﺘﻌﻤﻞ ﻓﻰ ﺍﻟﻌﺎﺩﺍﺕ ﻓﻘﻂ ﺩﻭﻥ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﺍﺕ »

«ZA'AI AMFANI DA WANNAN RUWA WAJAN AL'ADA KAWAI, BANDA IBADA»

.
٣ - ﺍﻟﻤﺎﺀ ﺍﻟﻨﺠﺲ .

3-RUWA MAI NAJASA (Wanda Najasa ta Fada masa)

.
« ﻭﻫﻮﻣﺎﺗﻐﻴﺮﺃﺣﺪﺃﻭﺻﺎﻓﻪ ﺍﻟﺜﻼﺛﺔ،ﺑﺸﻰﺀﻧﺠﺲ . ﮔﺎﻟﺒﻮﻝ،ﻭﺍﻟﻌﺬﺭﺓ
،ﻭﺍﻟﺨﻤﺮ،ﻭﻏﻴﺮﻩ »

«SHINE RUWAN DA DAYA DAGA CIKIN SUFFOFIN SA UKU SUKA JIRKITA DA WATA NAJASA kamar FITSARI, ko TUROSO (kashi), ko GIYA» da dai sauran su.

.
« ﻻﻳﺴﺘﻌﻤﻞ ﻓﻰ ﺷﻰﺀﻣﻦ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﺍﺕ،ﻭﻻﻓﻰ ﺷﻰﺀﻣﻦ ﺍﻟﻌﺎﺩﺍﺕ »

«BA'A AMFANI DA DAGA NAU'IN RUWAN NAN WAJAN IBADA, ko WAJAN AL'ADA» (za'a zubda shine kawai)

.
- ﻗﺎﻝ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺼﻼﺓﻭﺍﻟﺴﻼﻡ :
" ﺧﻠﻖ ﺍﻟﻤﺎﺀﻃﻬﻮﺭﺍ، ﻻﻳﻨﺠﺴﻪ ﺷﻰﺀ ﺇﻻﻣﺎﻏﻴﺮﻃﻌﻤﻪ،ﺃﻭﻟﻮﻧﻪ،ﺃﻭﺭﻳﺤﻪ " ‏( ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻰ )

Ma'aikin Allah...yace:
"AN HALICCI RUWA A TSARKAKE, WANI ABU BAYA MAIDA SHI NAJASA, SAI DAI IDAN YA JIRKITA DANDANAN SA, ko LAUNIN SA, ko KAMSHIN SA" (Nisa'i da Ibn maja).

.

ABIN NUFI:
Malamai Sun kasa Ruwa zuwa Nau'i uku:

-Nau'i na farko: shine Ruwan da yake kan Dabi'ar sa, wani Abu bai bata shi ba, wannan shi ake kira da (MUDLAKI), za'ai Amfani dashi wajan Ibada (Alwala) ko wajan Al'ada.(Girki) d.s

.

-Nau'i na biyu: shine Ruwan da wani Abu mai tsarki ya zuba a cikin sa, shi ake kira da (DAHIRI) wannan kuma za'ai Amfani dashi wajan Al'ada (girki) ba za'ai Amfanibdashi Wajan Ibada ba (Alwala).

.
-Nau'i na uku: shine Ruwan da wata Najasa ta Jikita Ainihin sa,shi wannan Ruwan ana kiransa (RUWA MAI NAJASA)
Ba za'ai Amfani dashi Wajan Ibada ko Al'ada ba.

.
___________ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻋﻠﻢ ___________ _

Allah yasa Abinda muka karanta ya Amfane mu Duniya da Lahira, ya kara mana So da Kaunar
Annabi....Sallallahu Alaihi wasallan

.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)