Kaka-kara-kaka: Babbar kotun tarayya ta aikawa da Jonathan sammaci

Bismillahirrahamanirrahim

Asalam  kukasance da Arewatricks  dan samun labarai

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake
zaman ta a garin Abuja babban birnin tarayya a
jiya Litinin ta bukaci ganin tsohon shugaban
kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya gurfana a
gabanta domin ansa wasu tambayoyi game da
shari'ar tsohon Sakataren jam'iyyar PDP Olisa
Metuh.

Wani babban jami'i a cikin mahukuntan kotun
ne da ya kwarmata ma wakilin majiyar mu
hakan a jiya inda ya bayyana cewa kotun ta
yanke shawarar yin hakan ne bisa ga bukatar
wanda ake tuhuma Olisa Metuh din.

Kaka-kara-kaka: Babbar kotun tarayya ta
aikawa da Jonathan sammaci

Arewatricks  haka zalika ta samu dai cewa bisa
bukatar kotun dai shine tsohon shugaba
Jonathan din zai gurfana ne a gobe Laraba
amma hakan ya dogara ne kacokan ga idan
an kaiwa tsohon shugaban takardar
sammacin cikin lokaci.

Mai karatu dai na iya tunawa cewa tsohon
Sakataren jam'iyyar adawa ta PDP na
fuskantar shari'a ne inda ake zargin sa da yin
facaka da makudan kudaden da suka kai
Naira miliyan 400 da ya ansa a hannun
Ibrahim Dasuki gab da zaben 2015.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)