Giyar Mulki babu abinda bata sawa, ta kan sa mutum ya guji yan uwa da abokan arziki, wasu kuma ta kan sa su kauce daga hanya, saboda a tunaninsu yanzu wuyar yayi kauri.

Dan kuka, ke ja ma uwarsa jifa: Yaron Sanata
Bala Ibn Na’Allah yayi kokarin kashe wani
Lamin da Ladaninsa, akan kiran Sallah

Giyar Mulki babu abinda bata sawa, ta kan sa
mutum ya guji yan uwa da abokan arziki, wasu
kuma ta kan sa su kauce daga hanya, saboda a
tunaninsu yanzu wuyar yayi kauri.
Wannan shine abinda ya faru a jihar Kaduna,
inda yaron Sanata Ibn Na’aAllah dake wakiltar
al’umman mazabar Kebbi ta kudu yayi
barazanar hallaka limanin Masallacin layinsu
dake titin Zobe road, cikin unguwar Rimi,
Kaduna da Ladaninsa, inji rahoton Jaridar
Dimokuradiyya.

ta ruwaito Yaron mai suna
Abdulmalik yayi yunkurin bindige Limamin ne
tare da Ladanin saboda a cewarsa wai suna
damunsa da yawan kiran Sallah, musamman
a lokacin da yake son hutawa.

Sanata Bala Ibn Na’Allah
Majiyar ta kara da cewa, Abdulmalik ya fito
daga gida cikin fushi dauke da bindiga, da
kuma wasu muggan karnuka suna take masa
baya, inda ya isa har kofar Masallacin, kuma
ya bayyana ma Limamin da Ladanin
bindigarsa tare da gargadinsu.
Wannan lamari ya faru ne gabannin sallar
Magariba a ranar Laraba 4 ga watan Oktoba,
inda a wannan lokaci da Abdulmalik ya fito,
ya gargade Malaman da su daina damun sa
da kiran Sallah, ko kuma zai dauki matakin da
ba zai yi musu dadi ba.
Wani shaidan gani da ido ya shaida ma
majiyar mu cewar a gabansa wannan lamari
ya auku, sa’annan ya kara da cewa wannan
ne Masallaci daya tilo akan titin Zobe na
Unguwar Rimi, wanda Limamin Masallacin
shine Malam Isah.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)