GANIN BUZU A MASALLACI YA ISA TINKIYA TAJI TSORON ALLAH*
GANIN BUZU A MASALLACI YA ISA TINKIYA TAJI TSORON ALLAH*
Wani Attajiri ya leqa tagarsa(window) sai yahangi wani Talaka yana tsintar abinci a cikin bolansa sai wannan mai kudi ya daga hannu sama yace *,"ALLAH NAGODE MAKA DA BAKAYINI TALAKA BA..."*
Bayan talakan ya gama ya kama hanyarsa ta zuwa gida, shi kuma sai ya hangi wani Mahaukaci yana tafe a kan titi tsirara,,, sai wannan Talakan ya daga hannu sama yace *,"ALLAH NAGODE MAKA DANA KASANCE TALAKA BA MAHAUKACI BA..."*
Shi kuma Mahaukacin yana karawa gaba sai yaga motar Asibiti ta dauko mara lafiya, sai ya yace *,"ALLAH NAGODE MAKA DAKA BANI LAFIYA..."*
Shi kuma mara lafiyan da aka kaishi Asibiti yaga gawa sai yace *,"ALLAH NAGODE MAKA DAKA BARNI DA RAINA..."*
Wato Mataccene kawai bazai iya godewa Allah ba sbd baida rai, mezai hana mu godewa Allah Yau akan Abubuwan daya bamu na jindadi da more rayuwa????
Ni Nagodewa Allah daya yini musulmi Ahlussunnah ya bani rai da lafiya da zaman lafiya da abunda lafiyar zataci...
*SHIN MENENE RAYUWA???*
In kanaso kasan wadannan amsoshi kai tsaye ka nufi wurare uku...
1→ Asibiti
2→ Gidan Yari
3→ Maqabarta
1→ Idan kaje Asibiti, ananne zaka gane ba abunda yafi lafiya mahimmanci agareka
2→ Idan kuwa kaje Gidan Yari ananne zakasan ashe 'Yanci yanada muhimmanci a wajenka
3→ Idan kajeka Maqabarta kuwa anan zaka fahimci ashe rayuwa bakomai bace...
Kasar da muke takawa a yau ita zata zamo dakinmu a gobe...
*MAGANAR GASKIYA*
Ba muzo da komai ba haka zamu koma bakomai...
Don haka mu tsaya muyi tunani sannan mugodewa Allah (s.w.a)
ALLAH yasa mudace Amin.
Comments
Post a Comment