FARKON HADUWANKA DA ALLAH

*FARKON HADUWANKA DA ALLAH*

*Farkon haduwanka da Allah shine yayin da aka rufeka a kabarinka, tabbas mutuwa ba itace abar tsoro ba, tsoron kam shine dame zaka hadu,

Yaya yanayin sabuwan rayuwanka kuma sabon wajen zamanka zai kasance,,shin guri ne da zaka more kaji dadi har kana   gwadayin ayi tashin kiyama domin kana hango makomarka mai dadi, ko kuwa sabanin Haka?....

dan uwa jin dadinka fa shine ayyukanka na alkair,,,,Shin anan gidan duniya zaka iya tuna abokinka Wanda kafi shakuwa dashi, ko kuwa matarka da kakejin dadin zama da ita kake sonta itama ke sonka?...A cikin kabari, Sallarka itace zata maye gurbinsu,,

idan ka rike sallah kuma kayita irin yadda manzon Allah ya koyar, to Insha Allah zaka samu jindadin zaman kabarinka...

wato mutane suna ganin kaman abinda ake fadi game da rayuwan kabari da tashin alkiyama ba zaizo ba,,,ka fa tuna manzon Allah ne ya fadi kuma nasan baka da shakka game da fadin manzon Allah, wallahi rayuwan duniya ba tabbas, kuma ba lallai sai baka da lafiya shine mutuwa ke riskanka ba,,

,shin baka taba jin labari ba cewa mutum yana cikin tafiya ya yanke jiki ya fadi daganan shi kenan babu rai,,,akwai cutuka wadanda kai kanka maishi baka San kana dasu ba a haka zasu taru su kar mutum,,,shin kasan cutar da aturance ake Kira HEART ATTACK?...

yan uwa muji tsoron Allah mu kyautata ayyukanmu, muyi koyi da sunnar manzon Allah,,,WALLAHI DUKKAN WANDA YABI ANNABI SAU DA KAFA, ZAI SHIGA ALJANNAH...Allah yajikan wadanda suka rasu, idan tamu tazo Allah ya sa mu cika da imani, Allah ya gafarta mana ya sanya Aljannah itace makomarmu baki daya*

Ka tura wasu groups din domin tunatar da yan uwa,,,,tabbas a cikin tunatarwa akwai lada

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)