Dalilin da yasa na karfafa wa Rahama Sadau gwiwa don taba gwamna Ganduje da Sarkin Kano hakuri – Ali Nuhu

Fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu ya
kasance mutumin da ya karfafa wa korarriyar
jaruma Rahama Sadau gwiwar ba gwamnan
jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da mai
martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II
hakuri kan al’amarin da ya kai ga dakatar da ita
daga masana’antar shirya fina-finan Hausa a
shekarar bara.

Ku tuna cewa kungiyar kula da ladabtar da
masu shirya fina-finai wato MOPPAN ta yanke
hukuncin korar jarumar bayan ta bayyana a
wani kasetin waka wanda bai dace ba tare da
mawakin Jos ClassiQ.

Ali Nuhu wanda yayi magana da jaridar Daily
Trust akan wayan tarho yayinda yake shirin
barin kasar ya bayyana cewa jarumar ta yanke
shawarar bayar da hakuri ne bayan ta gane
kuskurenta ya kara da cewa dan Adam ajizi
ne.

Dalilin da yasa na karfafa wa Rahama Sadau
gwiwa don taba gwamna Ganduje da Sarkin
Kano hakuri – Ali Nuhu
“A matsayinmu na manya a masana’antar shirya
fina-finai, hakki ne da ya rataya a wuyanmu
domin kula da na kasa damu wannan ne dalilin da
yasa na jajirce wajen bada hakurin ta.

A daren ranar Talata, 24 ga watan Oktoba, da
take magana a wani shirin gidan radiyo mai
taken “Ku Karkade Kunnuwan Ku” wanda ake
gabatarwa a shahararren gidan radiyo a garin
Kano, Radio Rahama, jarumar ta sha alwashin
cewa irin haka ba zai sake faruwa ba.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)