BAYANI KAN TSARKI

*BAYANIN TSARKI*

_tsarki kashi 2 neh:_
°Tsarkin kari
°Tsarkin dau'da

• Dukkan su basa inganta saida ruwa mai tsarki, mai tsarkakewa shine: wanda kamarsa bata jirkita ba, ko dandanon sa, ko qamshinsa, da abunda yake rarrabe shi marinjayi. Babu laifi da kasar gishiri da kasar kanwa da makamancinsa

• Idan najasa ta fito fili sai a wanke gurin, idanta fantsama sai a wanke tufar gabadaya. Wanda yayi kokwanto acikin samuwar najasa, to sai yayi yayyafi da ruwa ajikin kayan

• Idan kuma wani abu ya sameshi sai yayi kokwanto acikin najastuwarsa, to ba sai yayi yayyafi ba.

• Wanda kuma ya tuna da najasa yana cikin sallah sai ya yanke sallar, saidai idan yaji tsoron fitar lokaci. Wanda yayi sallah da ita yana mai mantuwa sai ya tuna bayan yayi sallama to ya sake sallah idan da lokaci.

Allah ya karbi Ibadunmu ya sa mu cika da Imani.

Rubutawa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.

_____________________________________

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)