Aljannu ne su ka aike ni da kudin, in ji wani da 'yan sanda su ka kama da jabun dalar Amurka

- 'Yan sandan Jihar Neja sun yi ram
da wani
mai suna Abubakar Suleiman, dauke da jabun
880,000 na dalar Amurka

- Suleiman ya ce shi dai dan aiken aljannu ne,
bai san kudin jabu bane

- Hukumar 'yan sanda ta ce Suleiman na cikin
kungiya masu yawo da kudin bogi wanda ta ke
nema ruwa a jallo




Abigail Unaeze, mai magana da yawun
Hukumar 'yan sandan Jihar Neja, ta ce 'yan
sanda sun yi ciki da wani Abubakar Suleiman
yayin da ya kai wa wani Injiniya Abdullahi
Sambo jabun 880,000 na dalar Amurka, a
yankin Shango na garin Minna.

Wani dan uwan Sambo mai suna Mamman
Manya ne ya kai Suleiman kara ofishin 'yan
sanda da ke Chanchaga. Suleiman dai ya
amsa laifin mallakar jabun kudi amma ya yi
ikirarin aljannu ne su ka umurce shi ya karbi
kudin a hannun wani mai suna Khalifa.

Aljannu ne su ka aike ni da kudin, in ji wani
da 'yan sanda su ka kama da jabun dalar
Amurka
Suleiman dai ya ce aljannun sun kira shi ne su
ka umurce shi ya karbi sako daga hannun
Khalifa, ya kai wa Sambo. Ya ce kuma sun yi
alkawarin zasu taimake shi da kudi, amma
baya ga wanann bayani, bai san komai ba

Suleiman ya kuma ce ya yi ta kiran khalifa ta
wayar tarho amma ya ki ya daga wayar ta sa.
Ita kuwa Hukumar 'yan sanda ta ce, Suleiman
ya na cikin wata kungiyar masu yawo da
kudaden boge ne wanda daman Hukumar ke
neman su ruwa a jallo.

Kukasance da Arewatricks

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)