AIYUKA KADAN MASU LADA MAI YAWA*

AIYUKA KADAN MASU LADA MAI YAWA*

Yana cikin falalar Allah akan bayinsa da kuma falalar da Allah ya sanyawa wannan al'umma ta Annabi Muhammad ﷺ,Allah ya sanya mata lokuta masu falala da aiyuka kada masu falala kamar,daren Laitul Qadri yafi daren watanni dubu falala da albarka ga ranar Arfa ga ranar juma  da sauransu,Allah yayi mana hakane dan mu samu kamo sauraran al'umma da kuma fifita al'ummar Manzon Allah
ﷺ akan sauran dukkan Al'ummomi baki daya.

*1-Manzon Allah ﷺ yana cewa:*

(Mafi soyuwar magana a wajan Allah,guda hudune:-

*(سبحان الله،والحمد لله،ولا إله إلا الله،والله أكبر"

SUBHANALLAH, WALHAMDULILLAH, WALA ILAHA ILLALLAH,WALLAHU AKBAR)* bazai cutar da kai daga duk wanda ka fara fada".

@رواه مسلم .

*2-Wanda ya karanta Qulhuwallahu Ahad sau goma,Allah zai gina masa gida a aljanna*

@صححه الألباني.

*3-Duk wanda ya nemawa mai Imani gafara,Allah zai rubuta masa lada ga kowane mai imani da ya nema masa gafara*

@حسنه الألباني. 

*4-Babu wani a bayan kasa da zai fadi;-*

*(لا إله إلا الله ، والله أكبر، ولا حول ولا
قوة إلا بالله "

LAA ILAHA ILLALLAH,WALLAHU AKBAR,WALA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH)*face sai Allah ya gafarta masa dukkan zunubansa koda sun kai yana kumfar teku"

@حسنه الألباني . 

*5-Idan bawa yace:-*

*"الحمد لله كثيرا"

ALHAMDU LILLAH KASIRAN*sai Allah yace;Ku rubutawa bawa Rahamata mai yawa"

@حسنه الألباني .

*6-Wanda yayi wannan Istighfarin yace;-*

*(أستغفر الله الذي لا إله إلا هو الحي
القيوم وأتوب إليه،

ASTIGHFIRULLAH ALLAZY LAA ILAHA ILLAHUL HAYYUL QAIYUM WA 'A TUBU ILAIHI)*ya fadi hakan sau uku,an gafarta masa laifukansa ko da gudune daga wajan yaki"

@صححه الألباني.

*7-Duk wanda ya roki Allah ya sanya shi aljanna sau ukku,sai Aljanna tace:*

*Ya Allah ka shigar da shi a aljanna*kuma duk wanda ya roki Allah ya kareshi daga shiga wuta sau uku,sai Wuta tace:

*Ya Allah ka tseratar da shi daga gareni*

@صححه الألباني .

*8-Duk wanda ya fadi:-*

*(سبحان الله العظيم وبحمده،

SUBHANALLAHIL AZIMI WABIHAMDIHI)*an dasa masa itaciyar Dabino a gidan Aljanna"

@صححه الألباني .

*9-Daga Ummu Rafi'an R.A tace,Ya Manzon Allah ﷺ,ka bani labarin wadansu yan kalmomi da zan riqa fada,amma kada ka tsawaità min?? Sai yace;

*(Ki ce: الله أكبر sau goma,سبحان الله sau goma sai Allah yace wannan nawane,kice اللهم اغفر لي sau goma sai Allah yace:hakika an aikata,tana sau goma Allah yana cewa har an aikata)*

@صححه الألباني.

        

Allah ne mafi sani

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)