ABUBUWA GUDA 6 DA YA KAMATA KA AIKATA IDAN AN KAWO MAKA GULMAR WANI
ABUBUWA GUDA 6 DA YA KAMATA KA AIKATA IDAN AN KAWO MAKA GULMAR WANI
Gulma da Annamimanci suna cikin abubuwan da suke sanyawa anyiwa mutum azaba a qabarinsa,kuma ya samin shiga azabar Allah a gobe alqiyama.yana da kyau kowa yayi kokari wajan kare mutuncin dan uwansa ta hanyar hana yaduwar gulma da cin naman yan uwanmu a tsakanin mu.
Imam Ghazaaly Allah yayi masa rahama yana cewa;
*"Dukkan wanda ya kawo maka gulma da annamimancin wani,sai yace maka,lallai wane yana fadar magana marar kyau akanka,wane yana aibantaka wane yana cin mutumcinka,ko yana bataka a idon jama'a.
Wanda ya fada maka wanna to akwai abubuwa guda shida a kanka.
*1-Na farko*
*'Kada ka gaskata shi acikin dukkan abinda ya fada,domin mai kawo maka gulma ko annamimanci fasiqine da lafazin Alqurani mai girma'*
Allah yana cewa:
(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِن جَاءَكُمْ فَاسِقٌ بِنَبَإٍ فَتَبَيَّنُوا أَن تُصِيبُوا قَوْمًا بِجَهَالَةٍ فَتُصْبِحُوا عَلَىٰ مَا فَعَلْتُمْ نَادِمِينَ)
(Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan fãsiƙi Yã zo muku da wani babban lãbãri, to, ku nẽmi bayãni, dõmin kada ku cũci waɗansu mutãne a cikin jãhilci, sabõda haka ku wãyi gari a kan abin da kuka aikata kunã mãsu nadãma).
الحجرات (6) Al-Hujuraat
*2-Na biyu*
*'Kayi masa nasiha ko wa'azi kuma ka hanashi cigaban yin hakan,tare da nuna masa munin abinda yake aikawa da sakamakon mai aikita haka awajan Allah'*.
Allah yana cewa:
(.......وَأْمُرْ بِالْمَعْرُوفِ وَانْهَ عَنِ الْمُنكَرِ).
(.....Kuma kayi Umarnin da kyakkyawan aiki kuma kayi hani daga mummunan aiki).
@[لقمان: 17].
*3-Na ukku*
*'Ka nuna masa fishinka saboda da Allah,saboda ya aikata abinda ya sabawa umarnin Allah,domin wanda yayi fishi idan an taba shari'ar Allah,to yana fishine da fishin Allah'*
*4-Na Hudu*
*'Kada ka munana zato ko zargin wanda aka kawo maka gulmarsa,kuma kada ka amince ko yarda da abinda aka fada game shi akanka'*
Allah yana cewa:
(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اجْتَنِبُوا كَثِيرًا مِّنَ الظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ الظَّنِّ إِثْمٌ ۖ وَلَا تَجَسَّسُوا وَلَا يَغْتَب بَّعْضُكُم بَعْضًا ۚ أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ أَن يَأْكُلَ لَحْمَ أَخِيهِ مَيْتًا فَكَرِهْتُمُوهُ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ تَوَّابٌ رَّحِيمٌ)
(Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nĩsanci abu mai yãwa na zato. Lalle sãshen zato laifi ne. Kuma kada ku yi bincin kwakwaf, kuma kada sãshenku yã yi gulmar sãshe. Shin, ɗayanku nã son yã ci naman ɗan'uwansa yanã matacce? To, kun ƙĩ shi (cin nãman). Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai karɓar tũba ne, Mai jin ƙai).
@الحجرات (12) Al-Hujuraat
*5-Na Biyar*
*'Kada abinda aka fada maka na gulmar wani ya sanyaka zuwa binci ke akansa da son sai ka gano ya fada ko bai fada ba'*
Allah ya hanamu yin binciken kwakwaf game da sanin halin yan uwanmu sai Allah yace:
(....وَلَا تَجَسَّسُوا وَلَا يَغْتَب بَّعْضُكُم بَعْضًا ۚ أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ أَن يَأْكُلَ لَحْمَ أَخِيهِ مَيْتًا فَكَرِهْتُمُوهُ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ تَوَّابٌ رَّحِيمٌ)
(...Kuma kada ku yi bincin kwakwaf, kuma kada sãshenku yã yi gulmar sãshe. Shin, ɗayanku nã son yã ci naman ɗan'uwansa yanã matacce? To, kun ƙĩ shi (cin nãman). Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai karɓar tũba ne, Mai jin ƙai).
@الحجرات (12) Al-Hujuraat
*6-Na shida*
*'Kada ka yarda da abinda wanda ya kawo maka gulma ya fada,kuma kada kaima kariqa yawo da maganar ko ka riqa tattauna maganar..'*
@[7505] ((إحياء علوم الدين)) (3/156).
.
Wani mutum yazo wajan;Aliyu Bn Husain Allah yayi masa Rahama,sai ya kawo masa gulmar wani mutum,sai Aliyu Bn Husain yace masa;Mu tafi zuwa ga wannan mutum,da suka je wajan wannan mutum sai yace;
*'idan abinda ka fada laifinane to Allah ya gafarta mini,idan kuma ba haka baneba Allah ya gafarta maka'*.
@[7506] ((الزواجر عن اقتراف الكبائر)) لابن حجر الهيتمي (2/571). .
Allah ne mafi sani
Allah ya nisantar da mu daga yada gulma da bata yan uwan mu musulmai.
Daga *MASJID DARUL QUR'AN*
Comments
Post a Comment