HAKKOKI 35 NA MUSULMI AKAN DAN UWANSA MUSULMI

Hakkoki 35 na Musulmi akan dan uwansa Musulmi.

Muna kula kuwa?

Daga Sheik Aminu Ibrahim Daurawa

1. Yayi masa sallama idan sun hadu
2. Yayi masa murmushi da faraa
3. Ya mika masa hannu su gaisa
4. Idan ya kira shi ya amsa
5. Idan bashi da lafiya yaje ya dubu shi
6. Idan ana binsa bashi ya taimaka masa wajan biya
7. Ya dinka kyautata atata masa zato
8. Ya zauna dashi lafiya
9. Ya bashi abinci idan yana Jin yunwa
10. Ya girmama dattijo musulmi
11. Ya tausawa yaro musulmi
12. Ya cika masa alkawari idan sunyi alkawari
13. Yayi masa sulhu da wanda suka sami rashin jituwa
14. Kada ya dinka tuhumar musulmi
15. Ya nema masa alfarma idan yana da wata bukata
16. Ya dinka girmama malamai da masu Ilmi
17. Yayi masa addua idan yayi atshawa
18. Idan ya nemi agajinka, ka agaza masa
19. Ya dinka yi masa addua da fatan alkhairi
20. Kada ya zalunce shi
21. Kada ya tabar dashi
22. Kada ya dinka yi masa hassada akan wata niima da Allah yayi masa
23. Ya girmama shi idan yazo masa a matsayin bako

24. raka janaizar sa. Idan ya mutu
25. Ya je kabarinsa domin ziyara da addua
26. Ya so masa abinda yake sowa kansa
27. kada ya cuci musulmi
28. ya zama Mai tawadiu ga kowa
29. kada yayi gulmar sa. ko yayi masa annamimanci
30. kada ya kaurace masa fiye da kwana uku
31. Ya kyautatawa dan uwansa musulmi
32. Kada ya shiga gidansa sai da izninsa
33. Ya umarceshi da kyakyawan halaye ya hanashi mummunan hali
34. Kada yayi ciniki akan cikinsa
35. Kada ya nemi aure akan auransa
36. Kada ya dinka yi masa bincike da bin diddiginsa

37. ya kubutar dashi idan yayi rantsuwa
38. Ya kiyayi mutunci da dukiya da jini na musulmi

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)