Dandalin Kannywood: Barayi sun haura gidan jarumi Suleiman Bosho

Labaran da muke samu daga masana'antar
Kannywood na nuni da cewa wasu bata garin
mutane sun haura a gidan fitaccen jarumin
fina-finan Hausa musamman ma a fagen
barkwanci watau Suleiman Bosho.

Haka ma dai kamar yadda muka samu daga
majiyar ta mu wannan mummunan lamari ya
faru ne a ranar Asabar din da ta gabata
amma sai dai mun samu tabbacin cewa
barayin ba su samu nasarar daukar wani
muhimmin abu ba mai anfani sosai daga
gidan.

Dandalin Kannywood: Barayi sun haura gidan
jarumi Suleiman Bosho

Majiyarmu ta samu dai cewa barayin da zuwa
yanzu bamu san adadin yawan su ba sun
haura ne cikin gidan da dare kuma suka shiga
wani daki suka hargitsa shi da nufin su samu
abun da suke so amma sai ba su samu ba.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan
baya ma dai mun kawo maku labarin cewa
jarumin ya koka da yadda a kullu yaumin
yake ta kara samun masu yi masa bakin ciki
da hassada da ma a wasu lokuttan kage.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

ASIBITIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)